Ɗaya daga cikin abubuwan da aka taɓo shi ne batun bidiyon da wata jarida ta fitar, inda ta yi iƙirarin cewa gwamnan Jihar Kano ne Abdullahi Ganduje yake karbar kuɗaɗen ƙasashen waje daga hannun wani mutum.
Lamarin da ya janyo cece-ku-ce, ba ma a jihar Kano kawai ba, har ma da Najeriya baki ɗaya, abin da ya kai ga majalisar dokokin jihar kafa kwamiti domin binciken gaskiyar lamarin.
Sai dai tun wancan lokaci gwamnan bai fito da kansa ya yi magana a kan zarge-zargen ba.
Amma a lokacin tattaunawarsa da BBC ta awa guda, wani daga cikin al'ummar jihar da suka halarci dakin tattaunawar ya yi tambaya da bukatar ganin gwamnan ya yi bincike kan lamarin, kasancewar yana ƙoƙarin ganin an yaƙi ayyukan rashawa a jihar.
A lokacin da ya yi tambayar, Kabir Dakata na Cibiyar Wayar da Kan Al'umma da Tabbatar da Adalci, KAJA, ya ce "An san mai girma gwamna ya ce zai ƙarfafa gwiwa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, me zai hana gwamna ya yi duk abin da zai yi domin ganin an bincika maganar zarge-zargen faya-fayen bidiyon Dalar nan domin a tabbatar da adalci a kansu?"
A lokacin da gwamnan ya amsa tambayar ya ce wannan bidiyo da aka fitar ba gaskiya ba ne, kuma ya ce ana bincike a kai kuma za a dauki mataki kan duk wanda ke da hannu.
Ya ce wadanda suka yi bidiyon sun yi ne a matsayin maƙarƙashiya domin hana shi shiga zaɓe, sai dai ba su ci nasara ba.
A ɓangare guda kuma gwamnan ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka da yawa a jihar, amma kuma a cewarsa har yanzu akwai sauran matsaloli da yawa.
Yana mai shaida cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka wadanda za a rinƙa tunawa da shi sama da shekara 100 masu zuwa
Ayyukan da gwamnan ya kafa hujja da su, su ne manyan gadoji da ya gina a birnin Kano, da kuma asibitin Muhammadu Buhari, wanda ya ce an sanya wa kayan kiwon lafiya na zamani.
A cewarsa asibitocin da gwamnatin tasa ta gina za su rage yawan mutane da ke zuwa ƙasashen waje domin neman magani.
'Abubuwa sun lalace a kasuwar Kantin-kwari'
A cewar gwamna Abdullahi Ganduje abubuwa da dama sun tabarbare a kasuwar kantin-kwari kafin zuwan gwamnatinsa.
Ya ce "Akwai cunkoso sosai, babu tituna, babu magudanar ruwa kuma mutane na kasa kaya a kan titi."
Sai dai a cewarsa bayan zuwan gwamnatinsa ne aka yi gine-gine irin na zamani, aka yi babban daki domin masu yin talla a kan hanya, aka yi tituna, kuma aka sanya tsaro.
A bangaren shugabanci na kasuwar kuwa, gwamnan ya ce tsarin da ake da shi a baya ba shi da inganci shi ya sa gwamnatinsa ke shirin samar da kyakkyawan tsari.
Wasu daga cikin ƴan kasuwar da suka koka game da shugabancin, kamar Sanusi Abubakar da Rabi'u Abubakar sun ce shugabancin da ake da shi a yanzu ya gaza wajen warware matsalolin da ƴan kasuwar ke fuskanta.
Sun yi zargin cewa wadanda gwamnati ta naɗa a yanzu domin shugabantar kasuwar ba su san matsalolin da ke addabar ƴan kasuwar ba.
Abin da ya sa ƴan china suka yi babakere a Kantin-kwari
A lokacin da gwamnan ya amsa tambaya game da koken ƴan kasuwar kan matsalar ƴan china a Kantin-kwari, ya ce za a ɗora laifin ne a kan ƴan kasuwa na cikin gida wadanda ke haɗa baki da ƴan china wajen sayar da kaya a kasuwar, a madadin ƙyale wa 'yan gida.
Haka nan kuma ya ce wata matsalar game da wannan batu ita ce yarjejeniyar cinikayya ta kasa-da-kasa wadda Najeriya ta sanya wa hannu, abin da ya bai wa mutanen ƙetare damar sayar da kaya a cikin Najeriya.
Sai dai a cewarsa ya tattauna da ƴan kasuwa na cikin gida, matakin da ake shirin dauka shi ne a hana irin wadannan ƴan kasuwa na cikin gida ci gaba da haɗa baki da ƴan china wurin sayar da kaya a kasuwar.
'Ina jin daɗi duk lokacin da aka yi kuka kan sayar da filayen gwamnati'
Wani abu da ke daukan hankali a jihar Kano shi ne koke-koke game da bayar da filayen wasu ma'aikatun gwamnati ga ƴan kasuwa.
Wani da ya aiko mana da saƙon bidiyo mai suna Lawal Jibril Magaji ya ce bai kamata a rinka sayar da filayen al'umma irin su gidan jaridar 'Triump' da gidan zakka da kuma Badala ba.
Ya ce 'Kakanninmu sun gina Badala babu Turoli babu Tarakata, abu ne da za mu kalla mu bar wa jikokinmu su kalla, su yi alfahari da kakanni.'
Ita kuma Rahama Abdulmajid wadda ta zo wurin taron ta ce wasu ƙasashe na amfani da kayan tarihi wajen samun kudin shiga, ta tambayi gwamnan ko mene ne gwamnatin jihar Kano ke yi wurin kare Badala a matsayin abin tarihi?
A lokacin da ya amsa tambayoyin gwamna Abdullahi Ganduje ya ce suna yin haka ne domin hana ɓata-gari mayar da irin wadannan wurare na shaye-shaye ko aikata laifi.
A cewarsa masu wannan ƙorafi ba su fahimci manufar gwamnati ba ne wurin aiwatar da wannan aiki.
A game da Badala kuwa, gwamnan cewa ya yi gwamnati na ƙoƙari ne wurin kare ta ba lalatawa ba.
Ya kuma ce filayen da gwamnati ta bayar a kusa da gidan zakka filaye ne na gwamnati ba na gidan zakka ba.
Gwamnan ya kuma ce a yanzu Badala tana ƙarkashin kulawa ne na gwamnatin tarayya ba jiha ba.
Sulhu ko amfani da ƙarfi kan masu garkuwa da mutane?
An tambayi gwamnan game da matsayarsa kan muhawarar da ake yi na cewa a yi sulhu da masu garkuwa da mutane ko a'a.
Gwamnan ya ce yana da ra'ayin a yi amfani da da sulhu da kuma ƙarfi kan ƴan fashin daji.
"Ya kamata a yake su to amma kuma idan an samu yanayin da wasu suka tuba, za su iya zama gada wajen daidaitawa idan an saci wasu."
Latsa nan domin kallon cikakkiyar tattaunawar BBC da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
A FADA A CIKA shiri ne na musamman da BBC Hausa ke kawo maku tare da tallafin gidauniyar MacArthur.