BBC Hausa of Wednesday, 2 June 2021

Source: BBC

Abin da ba ku sani ba kan sabuwar dokar kula da tsofaffi da Buhari ya ƙaddamar a Najeriya

Ana sa rai cibiyar za ta taimaka wajen inganta lafiya da rayuwar tsoffi a ƙasar Ana sa rai cibiyar za ta taimaka wajen inganta lafiya da rayuwar tsoffi a ƙasar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da Cibiyar Tsoffi ta Najeriya ranar Litinin.

Majalisar dokokin ƙasar ta amince da wata doka wadda ta goyi bayan kafa cibiyar wadda za ta taimaka ne wajen kula da al'amuran ƴan Najeriya da shekarunsu suka haura 70.

A lokacin bikin ƙaddamarwar, Buhari ya ce kafa cibiyar ya yi dai-dai da ɓangare na 16 (2) (d) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta inganta rayuwar tsofaffi a ƙasar.

Ana sa rai cibiyar za ta taimaka wajen inganta lafiya da rayuwar tsoffi a ƙasar sannan za ta yi rajistar duka mutanen da shekarunsu suka kai 70 a Najeriya.

Haka kuma, wasu abubuwan da za a samar a cibiyar sun haɗa da wurin motsa jiki da walwala waɗanda za su bai wa tsoffi damar more rayuwa.

Ana sa rai cibiyar za ta haɗa kai da gwamnatocin jihohi a faɗin Najeriya wajen samun cikakkun bayanan tsoffin.

Wani mutum mai suna Isa Adamu, mai shekaru 72 mazaunin jihar Kano ya shaida wa BBC cewa yana sa rai cibiyar za ta gyara rayuwar tsoffi a Najeriya.

"Muna jin labarin wasu ƙasashe ana cewa tsoffi na hawa motar bas kyauta kuma a shaguna ma su kan samu wasu abubuwan kyauta. Mu ma za mu so hakan."

"Muna fatan wannan sabuwar cibiya za ta inganta rayuwarmu yadda za mu san ana son mu kuma ana girmama mu kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen da suka ci gaba."

A Najeriya, mutanen da suka haura shekara 65 ne ake ce wa tsofaffi a hukumance kuma su ne kashi uku cikin ɗari na gaba ɗaya al'umar Najeriya.

Bincike ya nuna cewa Najeriya ba ta da wasu manufofi da ke aiki kan kula da tsofaffi, asali ma, karɓar kuɗin fansho na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da tsofaffi a Najeriya ke fuskanta.

Sai dai ana fatan cewa, kafa wannan cibiya zai taimaka wajen kawo ƙarshen wannan matsalar.