A baya-bayan nan, an samu ƙaruwar munanan hare-hare musamman kan ƴan sanda a jihohin kudu maso gabashin Najeriya da suka haɗa da Anambra da Imo da Ebonyi da Enugu da Abia da ma wasu jihohin kudi maso kudu kamar Rivers da Akwa Ibom.
Da fari, maharan sun fara ne da auka wa ɗaiɗaikun ƴan sanda musamman a inda suke aiki a shingayen duba motoci a kan tituna, su kashe su sannan su yi awon gaba da makamansu.
Daga baya sai suka ƙara ƙaimi suna kai hari ofisoshin ƴan sandan inda nan ma su kashe jami'an ƴan sanda su sace makamai - lamarin ya kai ƙololuwa da waɗannan mahara suka kai hari hedikwatar ƴan sanda a jihar Imo.
Sannan suka kai hari a wani gidan yari suka yi harbe-harbe kuma suka saki fursunoni sama da 1,700 duk a jihar Imo.
Haka kuma, sun kai jerin hare-hare a ofisoshin hukumar zaɓe ta INEC a ɓangarori da dama na yankin.
An sha alaƙanta waɗannan hare-hare da ƴan ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya amma kawo yanzu hukumomin Najeriya ba su tabbatar da hakan ba kuma ita ma ƙungiyar ba ta taɓa ɗaukar alhakin kai hare-haren ba.
Masana harkokin tsaro a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari inda wasu ke ganin cewa da irin waɗannan hare-haren ƙungiyar Boko Haram ta fara ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya.
Barista Audu Bulama Bukarti na Cibiyar Bincike ta Tony Blair da ke Burtaniya ya ce waɗannan hare-haren ba abu ne da ake yi ba da ka.
"Ana kai hare-haren nan ne bisa sani da kuma dabarar yadda za a yi a gurgunta yanayin tsaro a yankin sannan a lalata duk wani abu da gwamnati za ta iya amfani da shi wajen kama masu aikata laifin yadda za su ci karensu babu babbaka," a cewar Bukarti.
Bukarti ya bayyana cewa burin maharan ya fara cika a yanzu tun da ƴan sanda a wasu ɓangarorin yankin ba sa iya zuwa aiki da rigarsu ta aiki sai dai su sa kayan gida, ya ce wannan na kamanceceniya da yadda aka fara yaƙin Boko Haram.
"A farkon yaƙin Boko Haram, sai da ta kai mutanen gari ba sa bari ƴan sanda su zo kusa da su, hatta lauya da kayansa ke kama da na ƴan sanda gudunsa ake yi a wancan lokacin saboda suna gudun ka da ya goga masu kashin kaji," in ji shi.
Masanin ya ce idan wannan yanayi ya ci gaba a yadda ake, ƴan bindigar za su ci gaba da rusa gidajen yarin da ofisoshin ƴan sandan da suke ganin za a iya sa su idan an kama su sannan za su ci gaba da kashewa ko korar jami'an tsaron da za su kama su.
Ya ce wannan zai ba su dama su ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Mece ce mafita?
Bulama Bukarti ya ce lamarin ya fara ta'zzara amma gwamnati ba ta yi latti ba.
Ya ce yaƙin Boko Haram zai iya zama darasi ga gwamnatin Najeriya, ganin yadda ta yi yi sakwa-sakwa daga farko har lamarin ya lalace aka kai ga inda ake a yanzu.
"Kamata ya yi wannan shirin a yi masa tufka tun kafin wankin hula ya kai mu dare.
"Akwai buƙatar gwamnati ta matsa ƙaimi wajen amfani da ƙarfin soja da su ƴan sanda da jami'an leƙen asiri don tabbatar da cewa an yi bincike an gano inda suke ɓuya a kuma toshe hanyoyinsu na samun makamai da kuɗaɗe," a cewar Bukarti.
Sannan ya ce lallai ne gwamnati ta bi ƙa'idojin da suka dace ta dawo da shugaban ƙungiyar ta IPOB Nnamdi Kanu wanda a halin yanzu ya ɓoye a ƙasar waje don a yi masa hukuncin da ya dace.
"Su kansu gwamnoni da shugabannin al'ummar yankin kudu maso gabas ya kamata su koyi darasi. A lokacin da ƙungiyar Boko Haram ta fara kashe jami'an tsaro da jami'an gwamnati mutanen gari ba a ɗauka barazana ba ce a gare su.
"Wannan babban kuskure ne don mun ga abin da ya faru a arewa maso gaban.
"Haka kuma, idan aka duba sanarwar da ƙungiyar IPOB ɗin ta fitar na cewa kowa ya zauna a gida ranar Litinin alama ce da ke nuna cewa za su fara kai hare-hare kan al'umma.
"Sanarwar ta nuna cewa za su illata duk wanda bai bi wannan umarnin ba," in ji Bukarti.
Ya ce da wannan ne gwamnati za ta fara matsawa mutanen yankin cewa su fito a yi yaƙin da su, ta hanyar ba da bayanan sirri, idan suka ƙi jami'an tsaro su fara zargin cewa suna aiki ne tare da ƙungiyar su kama su ko su kashe su.
Idan kuma suka yi, su ƴan ƙungiyar su gansu a matsayin maƙiya ne su fara kai masu hare-hare, a cewar Bukarti.
Ya ce don haka dole ne shugabannin al'umma a yankin kudu maso gabas su farka su fahimci cewa abin da ke faruwa yanzu babbar barazana ce ga gaba ɗaya l'ummar yankin ba wai jami'an tsaro da jami'an gwamnati ba kawai.
Haka kuma, ya ce idan ba a yi wa tufkar hanci ba za ta yi wa yankin illa gaba ɗaya.
Bukarti ya ce "Ko ba komai, matakan da ƙungiyar IPOB take ɗauka da wanda gwamnati ke ɗauka sun fara shafar tattalin arzikin yankin da taƙaita ƴancin mutane na yin yawo da tafiye-tafiye kuma haka abun zai ci gaba da rurucewa kuma idan ya kai matuƙa mutanen ne za su wahala fiye da kowa."
Wane tasiri matsalar tsaron za ta yi ga zaɓen 2023?
Barrister Bukarti ya ce abubuwan da ke faruwa a jihohin Ibo za su yi mummunan tasiri ga zaɓukan 2023 da zaɓen da za a gudanar a jihar Enugu a ƙarshen shekarar nan.
Ya ce baya ga nan, rikicin na barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.
"Mun ga yadda mutanen nan suka matsa ƙaimi wajen kai hare-haren kan ofisohin hukumar zaɓe.
"Idan lamarin ya ci gaba nan da ƙarshen wannan shekarar ba za a iya zaɓe a jihar Enugu ba kuma idan abun yaƙara lalacewa har shekara ta 2023 ba za a iya babban zaɓe a jihohin yankin ba," a cewarsa.
Ya ce wannan zai iya gurgunta gaba ɗaya demuraɗiyyar Najeriya sannan zai iya haifar da sabon rikici domin ƴan yankin za su yi ƙorafin cewa ce an ware su ba a yi masu zaɓe ba a shekarar 2023.
Bulama Bukarti ya ce dole gwamnati ta yi dukkan mai yiwuwa don ganin an yi gaggawar shawo kan matsalar.
Waiwaye
A ƙarshen makon da ya wuce ne wasu ƴan bindiga suka harbe tsohon mai bai wa tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan shawara, Ahmed Gulak a jihar Imo a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama.
A ranar ne kuma rundunar ƴan sanda ta jihar Imo ta bayyana cewa ta kashe wasu mutum huɗu ƴan ƙungiyar IPOB da ta ce su ne suka kashe Gulak. Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri ne dangane da mutanen.
Washegari ranar Litinin, rahotanni suka bayyana cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe tsohon alƙalin babbar kotun jihar Enugu, Justice Stanley Nnaji.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun fitar da marigayin daga motarsa da ƙarfin tsiya sannan suka harbe shi sau da yawa har ya mutu.
Jami'an tsaro sun ce suna bincike kan kisan tsohon alƙalin.
Ƙarin labaran da za ku karanta:
- Igbo sun tsayar da al'amura don goyon bayan Biafra
- IPOB: Hotunan yadda kiran IPOB ya yi tasiri a jihohin Igbo