BBC Hausa of Saturday, 29 May 2021

Source: BBC

Abin da sabon farashin burodi a Najeriya ke nufi?

Farashin burodi tayi bisa saboda ƙaruwar farashin sinadaren haɗa burodin da dangoginsa Farashin burodi tayi bisa saboda ƙaruwar farashin sinadaren haɗa burodin da dangoginsa

Kungiyar masu burodi ta Najeriya ta umarci duka mambobinta da su ƙara farashin kayansu da kashi 30 cikin 100 saboda ƙaruwar farashin sinadaren haɗa burodin da dangoginsa.

Umarnin na zuwa ne ranar Alhamis bayan da aka cimma matsayar a ƙarshen tattaunawar majalisar zartarwar kungiyar da aka yi a Abuja.

Da yake bayani kan dalilan ƙara farashin, shugaban ƙungiyar na kasa Mansur Umar ya ce ƙaruwar farashin siga da bota da fulawa duka na cikin abubuwan da suka janyo ɗaukar matakin.

Shugaban ya ce farashin fulawar da suke saya a ƙasa da naira miliyan shida a duk mota guda, yanzu suna sayanta kan miliyan tara.

Nawa ne ƙarin da aka yi?

Cikin tattaunawarsa da BBC Hausa, mai magana da yawun ƙungiyar masu burodi, Kabiru Hasssan Abdullahi, ya ce an ƙara farashin ne da kashi 30 cikin 100.

"Kusan dukkan jihohi sun fara aiki da sabon farashin amma mu a Kano yau (Laraba) muka dawo, za mu kira taron masu gidan burodin," in ji shi.

Hakan na nufin burodin da ake sayarwa N100 zai koma N130. Na N200 zai koma N260, yayin da na N400 zai zama N520.

"Mu kanmu muna cikin matsala, idan ka duba gidajen burodin da aka rufe daga shekara ɗaya zuwa yanzu suna da yawa," in ji Kabiru Hassan.

"Mun yi iya 'yan dabarunmu don kar a ƙara amma babu yadda za mu yi, in ana son burodin ya fita da inganci dole ya fita da nauyinsa, shi ne zai zama lafiyayyen abinci."

Ya ƙara da cewa an samiu ƙarin naira 3,000 a kan kowane buhun fulawa cikin shekara ɗaya, wanda ya kai kusan kashi 50 cikin 100.

Gwamnati ta karya darajar naira a hukumance

Babban Bankin Najeriya ya karya darajar Naira da kashi 7.6 cikin 100 kan dalar Amurka, abin da masana ke ganin zai taka rawa wajen hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

Masanin tattalin arziki Dr. Muhammad Shamsuddeen na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce irin wannan matakin na lalata darajar kuɗi dama a kan talaka yake ƙarewa musamman tun da talaka ne yake zuwa kasuwa ya sayi kayan masarufi.

Ya ce kuma da yawa kayan masarufi a Najeriya shigo da su ake yi daga ƙasashen waje kuma wannan lalata darajar kuɗi zai shafi farashin kayan sannan ya ƙara tsawwala hauhawar farashi a ƙasar.

"Idan ba a manta ba a watan da ya gabata, hauhawar farashi a Najeriya ya kai kusan kashi 18.33 cikin 100, wanda yanzu idan aka ci gaba da lalata darajar Naira, hauhawar farashin na iya kaiwa kashi 20 cikin 100 nan da watan gobe" a cewarsa.

Dokta Shamsuddeen ya ce wannan shi ne babbar wahala da talaka zai iya fuskanta.

Ya ƙara da cewa lalata darajar Naira na iya haifar da rashin aikin yi a ƙasar tun da kamfanoni da masana'antu da dama a Najeriya sun dogara ne da shigo da kaya daga kasashen waje domin sarrafawa - wannan na iya nufin injina ko kayan da ake sarrafawa don samar da wasu kayayyakin.

"Idan ya zama cewa waɗannan kayayyakin sun yi tsada sakamakon faɗuwar farashin Naira, babu shakka wasu masana'antun ba za su iya ci gaba da aiki ba dole su rufe masa'antun ko su rage kayan da suke yi," in ji Dokta Shamsu.

Ya ce wannan zai haifar da korar mutanen da suke aiki a waɗannan masana'antun.