BBC Hausa of Saturday, 24 April 2021

Source: BBC

Abin da ya sa fursunoni suka yi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano

Wasu fursunoni sun yi  yunkurin tserewa sakamakon wata hatsaniya da ta barke a gidan Wasu fursunoni sun yi yunkurin tserewa sakamakon wata hatsaniya da ta barke a gidan

Wasu fursunoni a daya daga gidajen birnin Kano da ke arewacin Najeriya sun yi yunkurin tserewa sakamakon wata hatsaniya da ta barke a gidan.

Wasu bayanai sun nuna cewa fursunonin da ke gidan gyaran hali na Kurmawa sun yi yunkurin tserewa ne bayan da suka yi zargin cewa hukumomin gidan sun cuce su a kan kayan azumin da wasu attajirai suka kai gidan domin a raba musu.

Sai dai hukumar gidajen yarin ta yi zargin cewa hatsaniyar ta samo asali ne daga bangaren da aka daure fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisan kai.

Kakakin gidajen gyaran hali na jihar ta Kano, Musbahu Lawan, ya shaida wa BBC cewa sun gano an shigar da kayan laifi - wadanda suka hada da miyagun kwayoyi da wayoyin salula- zuwa bangaren fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisan kai su 150 inda jami'ansu suka kwace kayayyakin.

A cewarsa, dagewar da fursunonn suka yi cewa sai an mayar musu da kayan ne ya haifar da hatsaniyar.

"Jami'anmu kwararru a bangaren kwantar da tarzoma saun bi hanyoyin da doka ta tanada na ganin cewa an lallaba su sun shiga dakunansu," in ji Musbahu Lawan.

Ya kara da cewa hukumar kula da gidajen gyaran hali ta jihar ta Kano ta kafa kwamiti da zai yi bincike domin gano wadanda suka kitsa yunkurin fasa gidan yarin yana mai cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

Yunkurin fasa gidan yari ba sabon abu ba ne a Najeriya, inda ko a farkon watan nan sai da wasu da ake zagi masu fafutukar ballewa daga Najeriya ne na kungiyar IPOB suka fasa gidan yarin Owerri babban birnin jihar Imo kana suka kubutar da fursunoni.

Hukumomi sun sha cewa suna daukar matakai domin dakile irin wannan yunkuri musamman ta hanyar rage cunkoso a gidajen yarin da kuma tabbatar da ganin ba kowanne mai laifi ba ne aka kai shi gidan na yari.