BBC Hausa of Thursday, 3 June 2021

Source: BBC

Abin da ya sa muka dakatar da kai albasa Kudancin Najeriya – Kungiyar dillalan albasa

Yawan albasan da ke zuwa Kudancin Najeriya a Arewa ake noma su Yawan albasan da ke zuwa Kudancin Najeriya a Arewa ake noma su

Ƴaƴan ƙungiyar dillalan albasa a Najeriya da ke kai wa kudu maso gabashin kasar sun janye jigilar albasa zuwa yankin har sai abin da hali ya yi.

Sun ce matakin ya zo ne bayan wasu mutane da ake zargin masu rajin a-ware ne na ƙungiyar IPOB ɗauke da bindigogi suka tsayar da manyan motocin albasa biyu kuma suka sayar wa mutanen yankin kan naira dubu tara duk buhu maimakon naira dubu goma sha biyar.

Alhaji Halilu Muhammad Jaɓɓe, mai albasar da aka yi wa ɓarna a kudu maso gabashin Nijeriya ya bayyana wa BBC cewa a lokacin da aka kai wa moocin hari, jami'an tsaro sun kai musu dauki inda kuma su ka yi ta bata kashi tsakaninsu da mutanen da ake zargi da kai harin.

A cewarsa, sun yi asarar albasar da kudinta ya kai fiye da naira miliyan 13.