BBC Hausa of Thursday, 15 April 2021

Source: BBC

Abin da ya sa tallafin $30m bai hana sace ɗalibai bayan na Chibok ba a Najeriya

Tsohon Firai ministan Burtaniya, Gordon Brown, ya jagoranci shirin tara $ 30m Tsohon Firai ministan Burtaniya, Gordon Brown, ya jagoranci shirin tara $ 30m

Satar daruruwan 'yan mata' dalibai a makarantar Chibok, a Najeriya, yau shekaru bakwai cif cif da suka gabata, Ta kai ga bullo da wani shiri na miliyoyin daloli wanda wani tsohon Firai ministan Burtaniya ya goyi baya don karfafa tsaro a makarantu, amma nasarorin da aka samu ba su da yawa.

Manyan mutane da dama sun ta yin tururuwa zuwa makarantar ta Chibok don nuna alhini da kuma jajantawa dangin daliban da aka sace.

Ngozi Okonjo-Iweala, ministar kudin Najeriya a lokacin kuma a yanzu haka shugaban kungiyar kasuwanci ta duniya ta samu tarba daga shugabannin al'umma da iyayen da aka sace 'ya'yansu a Chibok.

Misis Okonjo-Iweala ta je Chibok ne don aza harsashin wani aiki na gyara makarantar Sakandaren Gwamnatin da mayakan Boko Haram suka lalata a wannan mummunan daren a watan Afrilun 2014.

Ta gabatar da takaitaccen jawabi, sannan kafin daga bisani ta yi abin da ya kai ta.

An yi musabaha da kuma hotuna da mahalarta taron, kama daga bisani ta kama hanya ta tafi.

Kasancewarta a can wani bangare ne na martanin hukumomi dangane da lamarin da ya faru.

Biyo bayan sace daliban da dama da aka yi ne kuma, sai duniya ta yi wa abin caa !, ta hanyar amfani da taken #BringBackOurGirls.

Don amsa kiran cewa dole ne a yi wani abu, tsohon Firai ministan Burtaniya, Gordon Brown, ya jagoranci shirin tara $ 30m tare da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da gwamnatin Najeriya da shugabannin 'yan kasuwa masu zaman kansu da manufar inganta neman ilimi hankali kwance.

An tsara cewa za a kare makarantu dari biyar, sannan za a samar da sabbin ajujuwa, za kuma akewaye makarantun, da kuma samar musu da masu gadi.

"Manufar shirin ita ce samar da yanayi mai kyau don koyo, ba tare da wata fargaba ba" in ji Mista Brown a watan Mayu 2014

Hakan ya yi kyau sosai, amma shekaru bakwai zuwa yanzu ba a samar da kariya ga makarantun 500 ba, ba a kare su ba kuma ba a gina ajujuwan ba.An samu wasu nasarori ciki har da samar da ajujuwan karatu da kayayyakin koyo ga yara a sansanonin mutanen da suka rasa muhallinsu, amma akasarin shirin an yi watsi da shi kasa da shekaru biyu bayan kaddamar da shi a Abuja.Yawaitar sace-sacen 'yan makaranta a Najeriya ya nuna gazawar gwamnati wajen samar da manufofi da za su inganta tsaro a makarantu.

Har yanzu an kasa gano yara ɗari da goma sha biyu daga cikin 'yan matan makarantar Chibok, ba kuma ba a sake gina makarantar su ba.Kodayake an kafa tubalin ajujuwa bayan ziyarar Misis Okonjo-Iweala, shugabannin al'umma sun ce ba a gina su sosai ba.

"Ginin bai da inganci, duk lokacin da aka yi iska sai ta rushe wani bangaren, na ginin. har yanzu yana ta rugujewa ko amfani da su ma ba a fara yi ba har yanzu" kamar yadda kakakin kungiyar iyayen yaran Chibok ya shaida wa BBC.

Duk da haka, a halin yanzu sojojin Najeriya suna gyara ajujuwan makarantar, wanda gwamnatin jihar Borno ta biya bayan Gwamna Babagana Zulum ya ziyarci makarantar a watan Nuwamba kuma abin da ya gani ya firgita shi.

Har ila yau, mutane da dama na jefa ayar tambaya a kan ko samar da katanga ga makarantun na iya kare su daga harin Boko Haram ?, domin hatta lokacin da aka kai hari makarantar Chibok ma akwai katanga.

"Zagaye makaranta da katanga na iya kare ta, amma babu tabas," in ji masanin tsaro Aminu Bala.

"Tsaron makarantu ya wuce zane na kayan kwalliya, idan akwai rashin tsaro gaba daya to da wuya a samu tsaro a ko'ina, musamman wurare masu rauni kamar makarantu," in ji shi.

Ofishin Burtaniya na Kasashe renon Ingila, ya shaida wa BBC cewa aikinsu shine aikinsa shi ne samar da "kwararan shawarwari kan hanyoyin bayar da kariya ga makarantu", gami da "bunkasa tsare-tsaren makarantu masu aminci"

Amma ya kara da cewa ba shi da alhaki kai tsaye na aiwatar da ayyukan saboda wannan yana karkashin rundunar sojojin Najeriya ne.

Sojojin Najeriya ba su amsa tambayoyin BBC ba game da yadda suke gudanar da aikin.

'Gwamnatin Najeriya ce ke tafiyar da aikin

Ofishin Mista Brown, wanda har yanzu shi ne wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan harkokin ilimi, ya shaida wa BBC a cikin wata sanarwa cewa "bayan sace-sacen 'yan kwanakin nan a shekarar da ta gabata, ya yi wata ganawa da ministar kudin Najeriya a shekarar 2020 don taimakawa a karfafa tsaro a makarantu.

Ofishinsa bai amsa tambayoyin game da yadda aka kashe $ 30m na farko ba, yana mai cewa "duk kudaden an bayar da su ne ta hanyar kulawar gwamnatin Najeriya".

Goodluck Jonathan, wanda a karkashin kulawarsa aka sace 'yan matan aka kuma kaddamar da wannan shirin da ake kira SSI, ya fadi, a zaben shugaban kasa na 2015, inda Muhammadu Buhari ya samu nasara.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da masu ba da tallafi na kasa da kasa sun ce tarurruka da ba a saba gani ba da kuma sauya manufofi da Mista Buhari ya yi ya kawo cikas ga ayyukan shirin tare da kai su ga ficewa.

A cikin rahoton nasa, Ofishin jakadancin na Burtaniya ya zargi gwamnatin Buhari da jinkiri wajen aiwatar da shirin na SSI tare da dage tarukan tattauna batun saboda tarurrukan kwamitocin da ba su dace ba.

An kuma nuna damuwa game da yadda Najeriya ke tafiyar da asusun da kuma manufofin Burtaniya cewa babu wani kudin tallafi da ya isa kai tsaye ga gwamnatin Najeriya.

Fadar shugaban Najeriya ba ta amsa tambayoyi game da wadannan batutuwa ba, ita ma ma'aikatar kudi da ke kula da asusun SSI ta ki cewa ko uffan.

Yanzu haka ana shari'ar wani tsohon mamba a gwamnatin Buhari, Babachir Lawal, wanda ofishin sa ya samu damar shiga asusun SSI, saboda zarginsa da laifin karkatar da naira miliyan 500 don sare ciyawa, zargin da ya musanta.

Yawan makarantu da aka rufe yanzu haka a arewa maso yammacin Najeriya saboda ayyukan masu aikata laifi, baya ga daruruwan da suka kasance a rufe na tsawon shekaru a arewa maso gabas, wata kila manuniya ce cewa bayan abin da ya faru na Chibok babu wata dabara ta dogon lokaci da za a yi don kare dalibai.

Ga kungiyoyi irin su Boko Haram wadanda ke adawa da ilimin boko, ci gaba da rufe makarantu, musamman ma na Chibok, na iya zama tamkar nasara ce.