An dade ana yi wa miliyoyi allurar rigakafi a faɗin duniya ta hanyar soka musu allurar a dantsen hannunsu da ke dab da kafaɗa.
Haka abun yake yayin da ake ci gaba da gudanar da rigakafin annobar korona a faɗin duniya.
To amma me yasa ake allurar rigakafi a dantse? Me yasa ba a yi a jikin fata kai tsaye ta hanyar jijiya, ko kuma ta hanci tunda tanan ne ake tunanin an ɗauki cutar?
Amma kuma a wasu kasashen kamar Amurka an aminta da a rika fesa rigakafi ta hanci musamman wanda ya shafi mura wato Flu vaccines.
Sai dai wasu kasashen kamar Australia kwata-kwata basu amince da fesa rigakafi a hanci ba.
Duk da haka akwai dalilai masu karfi da suka sa ake yin allura a dantse a maimakon sauran wurare da ke jikin ɗan adam.
ƙarfin dantse
Ba kamar sauran kafafen jiki ba, dantse na da ingantattun hanyoyin da jini ke gudana ba tare da tsaiko ba, wanda hakan yana taimakawa rigakafi wurin saurin narkewa cikin jiki, a cewar Joanna Groom, wata mai bincike kan garkuwar jiki a cibiyar nazari ta Walter da Eliza da ke Australia.
Dantse na dauke da wasu kwayoyin halitta masu ƙwari da ake kira dendritic cells, kuma suna da inganci wurin gudanar da aiki.
''Saboda haka Dendritic cells na taimakawa sosai wurin harba duk wani abu daga dantse zuwa sauran jiki,'' a cewar Dr Groom.
Rigakafin Covid-19
Dr Groom ta kara da cewa ''babu bambanci da rigakafin annobar korona da yanzu haka ake ci gaba da aiwatarwa a fadin duniya, don kuwa baya ga samar da kwayoyin halitta na dendritic, dantse na taka rawa a matsayin wani asusu da allurar rigakafi kan iya zama na tsawon lokaci ba tare da wata matsala ba.
Hakan ya kan sa garkuwar jiki ya shirya karɓar rigakafin ba da takura ba.
Bugu da kari rigakafin da ke shiga hanyoyin jini kai tsaye ka iya haifar da matsala.
''Akwai kuma wasu kwayoyin halitta da aikinsu shine daukar rigakafi da ke shigowa ta kafar dantse, kafin su raba shi a hankali zuwa ilahirin jikin dan adam'', a cewar Dr Groom.
Bayan haka kuma Dr Groom ta ƙara da cewa ''yin allurar rigakafi a dantse ba shi da hadari sosai, kuma da wahala ya saka wurin da aka yi allurar kumburi, ba kamar a sauran wuraren da ake iya yin allura ba''.
Kuma bincike ya nuna cewa yin rigakafin ta dantse ya fi sauƙin haɗarin kamuwa da rashin lafiya.
Wani muhimmin abu shine ''a duk lokacin da mutum ya kamu da wata rashin lafiya bayan yin allurar rigakafi na wani dan lokaci, wata alama ce da ke nuni da cewa garkuwar jikin ɗan adam na aikinta yadda ya kamata, saboda haka ba abin damuwa bane,'' inji Dr Groom.
''Dama ba abin mamaki bane yanayin mutum ya sauya idan aka yi masa allurar rigakafi, ba a cikin jiki ba kawai har ma a zahiri. Wani lokaci dantse zai yi ja ko kuma ya kumbura, to amma hakan na nufin garkuwar jikin ɗan adam na aikinta yadda ya dace.''