An kaddamar da kyaftin din kungiyar kwallon kafar Super Eagles Ahmed Musa a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tsohuwar kungiyarsa.
Ahmed Musa ya rattaba hannu na sake zama dan kungiyar ta Kano Pillars ne a wani mataki na karfafa gwiwar kungiyoyin da ke gasar lig-lig a Najeriya, kuma an gudanar da bikin kaddamar da dan wasan a ranar Alhamis a filin wasa na Kano Pillars da ke birnin Kano.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Alhaji Surajo Lawal Jambul ne ya mika wa kyaftin din kungiyar Super Eagles din rigar 'yan kwallo mai lamba 7 a yayin bikin kaddamarwar,
Dan wasan mai shekara 28, wanda ba ya buga wa kowacce kungiya tamaula tun da ya bar Al Nassr ta Saudiyya a watan Oktoba, ya samu tayin tafiya Ingila da Rasha da kuma Turkiyya.
Sai dai a yayin da yake nazari kan matakin da zai dauka na tafiya wata kasar Turai a bazara, dan wasan ya karbi goron gayyata daga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Shehu Dikko, shugaban League Management Company (LMC) domin ya murza leda a Pillars.
Tsohon dan wasan na Leicester City ya shaida wa BBC Sport Africa. cewa: "Bayan na yi magana da gwamna da shugaban LMC ina duba yiwuwar murza tamaula a Kano pillars."
"Zan yi duk abin da zai fito da mutuncin kwallon kafar Najeriya kuma ina kallon Kano Pillars da matukar muhimmanci.
Dan kwallon ya kuma ce: "Ita ce kungiyar da ta taimaka mini na zama shahararren dan wasan kwallon kafa a yau, don haka wannan dangantaka ta wuce ta kwallon kafa danganaka ce mai yauki."
Musa, wanda ya bude gidajen koyon kwalon kafa da atisaye biyu a arewacin Najeriya, ya ci wa Kano Pillars kwallaye 18 lamarin da ya sa ta yi nasarar lashe kofin lig na Najeriya a kakar wasan 2009/10.
Musa ya buga wa Najeriya kwallo sau his 96 inda a wasansu na baya bayan nan Super Eagles ta doke Lesotho da ci 3-0 a birnin Lagos inda ta samu gurbin zuwa gasar cin Kofin Nahiyar Afirka.
Gwamnatin jihar Kano ce ke da mallaka da kuma tafiyar da kungiyar wasan kwallon kafar ta Kano Pillars din wacce aka kafa a shekarar 1990.
Nasarorin da ya samu a Rasha da Saudiyya
Musa ya zura kwallaye 11 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 14a wasanni 57 da ya buga wa Al Nassr, tun da ya koma can daga Leicester City a bazarar 2018, abin da ya sa suka lashe kofunan Saudi Pro League da Super Cup.
Kazalika ya yi nasara a Rasha lokacin da ya murza leda a CSKA Moscow inda ya lashe kofunan lig-lig guda uku da kuma kananan kofuna uku, kafin ya tafi Leicester City a watan Yulin 2016.
Musa ya gaza taka rawar gani a Leicester inda ya ci mata kwallaye biyar a wasanni 33.
Duk da yake West Brom ta kasa daukarsa saboda batun kudi, ana rade-radin cewa Musa zai koma Firimiya Lig ta Ingila ko CSKA Moscow, inda ake matukar girmama shi saboda kwallaye 61 da ya ci mata sanna ya taimaka aka ci kwallaye 33 a wasanni 184 da ya buga.