Malaman addinin Musulunci da likitoci a Birtaniya sun tashi tsaye wajen kira ga Musulmi da su tabbatar sun ci gaba da zuwa ana yi musu allurar riga kafin korona a lokacin azumi, da cewa yin allurar ba zai karya musu azumi ba.
A lokacin azumin Ramadana da za a fara mako mai zuwa, Musulmi na kaurace wa abinci da ababan sha, da sauran abubuwa da aka haramta yi a yayin ibadar da rana.
Tuni ma dai wasu cibiyoyin da ake riga kafin a Birtaniya suka kara tsawon lokacin aikinsu, domin ba wa Musulmi damar zuwa a yi musu allurar bayan buda baki.
Malaman addinin Musulunci da ke kan gaba wajen wannan fadakarwa da k likitoci don ganin alumar Musulmi a BIrtaniyar sun ci gaba da zuwa ana yi musu riga kafin na korona, na bayar da fatawar cewa, yin allurar ba abu ba ne da zai karya musu azumi ba.
Saboda a fadar daya daga cikinsu Sheik Qari Asim, wani limami a Leeds, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kasa na bayar da shawara na kungiyar Masallatai da Limamai a Birtaniya, idan aka yi wa mutum allurar ruwanta zai bi cikin jijiya ne, ba cikin jinni ba,.
Saboda haka ba abu ba ne da zai kasance kamar abinci ga jikin mutum, kasancewar a bisa dokar Musulunci, mai azumi ba zai ci ko ya sha wani abu na abinci ba a lokacin da kuma aikata wasu abubuwa da aka haramta ga mai azumin.da rana, har sai bayan faduwar rana.
Wannan fatawa ita ce yawancin malamai suka tafi a kai kamar yadda Sheik Asim ya sheda wa BBC.
Malamin ya ce, sakonsa ga al'ummar Musulmi shi ne, '' idan har ka cancanci a yi maka riga kafin na korona, kuma an aiko maka da gayyatar ka je a yi maka, to sai ka tambayi kanka.
''za ka je a yi maka allurar ne wadda an tabbatar da amfaninta ko kuma za ka bari ne ka fuskanci hadarin kamuwa da cutar, wadda za ta sa ka rashin lafiya sosai, har ma ta iya sa ka kasa yin azumin na Ramadana gaba daya, a karshe ma ka kare a asibiti?''
Kasancewar wasu cibiyoyin allurar riga kafin koronar a Birtaniyar sun kara tsawon lokacin aikinsu ta yadda Musulmi za su iya zuwa bayan sun buda baki a yi musu, wata babbar likita daga yankin gabashin birnin Landan Dr Farzana Hussain, ta ce ai ba bukatar sai Musulmi masu azumin sun kaurace wa zuwa allurar da rana.
Ta ce, sun san cewa Musulmi da dama sun damu a kan yin allurar a lokacin azumin Ramadana, saboda da dama suna ganin yin allurar zai karya musu azumi, ta ce ko alama ba haka abin yake ba, domin allurar ba matsayin abinci take ba.
Dakta farzana ta kara da cewa Al Qur'ani mai girma y ace cetar ranka shi ne abu mafi muhimmanci: ' cetar rayuwar mutum daya tamkar ceton rayuwar al'umma baki daya ne, saboda haka nawi ne da ya rataya a kan kowa ne Musulmi ya yi riga kafin.
Domin karfafa wa jama'a yin riga kafin wasu masallatan ma an sa su a matsayin cibiyoyin yin rigakafin na korona a Birtaniyar.
Duk da cewa an bayar da damar yin sallar jam'i ko jama'a tare a fadin kasar ta Birtaniya, amma ba za a hada sahu ba, dole ne a yi nesa-nesa da juna, kuma 'yan wani gida ba za su hadu da na wani gidan ba a wuri guda rufaffe ba su yi salla, kasancewar a lokacin azumin ana sallah tare musamman ta asham.
A dangane da haka ne ma kungiyar likitoci Musulmi ta Birtaniyar ta fitar da wasu tsare-tsare ga masallatai a lokacin azumin. Daga ciki sun bayar da sahawara da a takaita tsawon sallar Tarawee, a tabbatar an bude tagogi yadda za a samu iska na shiga da fita sosai, kuma limamai su tabbatar sun sa takunkumi mai ninki biyu da zai zauna a fuskarsu sosai domin kare lafiyar mamu; wato masu bin sallah.
Dr Shehla Imtiaz-Umer, wata likita a Derby ta sheda wa BBC cewa: " Mun ga illoli da dama a cikin al'ummarmu saboda annobar korona, saboda haka muke kokarin tabbatar da ganin ba a sake ganin hakan ba a lokacin azumin Ramadana a gaba.
Ta ce, '' Abin takaici lamarin ya shafi azumin bara da kuma na bana. Amma idan muka ci gaba da karbar allurar rigakafinmu, kuma mu tabbatar da cewa mun kiyaye da dukkanin matakan kariya, za mu iya tabbatar da cewa al'amura sun komo akalla kusan yadda suke a watan Ramadana na gaba''.