BBC Hausa of Friday, 23 April 2021

Source: BBC

An ɗaure marubucin da ya yi ɓatanci ga addinin Musulunci a Algeria

Said Djabelkhir Said Djabelkhir

An yanke wa wani marubuci ɗan Algeria hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan kaso, kan ɓatanci ga addinin Musulunci.

Shari'ar Said Djabelkhir ta ja hankalin duniya.

Ɗan jaridar mai shekara 53, wanda yake da digiri a fannin addinin Musulunci, ya wallafa littattafai biyu a kan Musulunci.

An gurfanar da shi gaban shari'a bayan wasu lauyoyi biyu da farfesa sun shigar da ƙara kan kalaman da ya yi a shafukan sada zumunta.

Mutumin ya ce yankan dabbar layya da ake yi bisa tsarin addinin Musulunci ɗabi'ar marasa addini ce.

Ya kuma ce wasu sassan Al-Ƙur'ani kamar labarin Jirgin Annabi Nuhu, ba lallai ne ya kasance gaskiya ba, sannan ya soki yadda ake wasu abubuwan a Musulunci kamar auren wuri ga yara a wasu yankunan Musulmai.

Karkashin dokokin kasar Algeria, batanci ga Annabi Muhammad SAW ko addinin Musulunci babban laifi ne da a kan yanke hukuncin zaman gidan yari daga shekara biyar zuwa sama.

Musulmai sun yi imani da yankan dabba a lokacin Sallar Layya domin tuna wa da kyakkyawar niyyar Annabi Ibrahim ta yin sadaukarwa da ɗansa Annabi Isma'il a matsayin abin hadaya, a lokacin da Allah Ya yi masa umarni da hakan.

Bayan yanke hukuncin, da bayar da belin Djabelkeir, ya shaida wa manema labarai a wajen kotun da ke babban birnin kasar wato, Algiers, cewa yana shirin ɗaukaka kara saboda yana da 'yancin fadin albarkacin bakinsa.

An ruwaito shi a kafofin yaɗa labarai yana kira ga a sake yin nazari kan wasu bayanai da ke cikin Ƙur'ani da Hadisai.

Ya kuma masu sukarsa sun yi amanna cewa duk abin da ke cikin Ƙur'ani gaskiya ne, kuma ba sa bambance tsakanin "tarihi" da "camfi" - tamkar labarin Jirgin Annabi Nuhu.

A baya-bayan nan ya shaida wa AFP cewa "koyarwar Ƙur'ani ba ta dace da hasashe da buƙatun mutanen zamani ba."

Musulmai sun yi imani da Ƙur'ani zancen Allah SWT ne, kuma an saukar wa Annabi Muhammad SAW ne a matsayin hanyar rayuwar ɗan adam.

Ministan Harkokin Addini na Aljeriya Mohamed Aissa ya sha sukar Mr Djabelkhir, yana mai cewa ba zai bari "wani ya kawo ruɗani a ƙasar ba."

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da 'yan siyasa sun nuna goyon baya ga Djabelkeir, tare da cewa hukuncin da aka yanke masa ya take hakkinsa da 'yancin fadin albarkacin baki.

Lauyansa Moumen Chadi, ya ce ya kaɗu da hukuncin da aka yanke masa, ya ƙara da cewa ya yi tsammanin za a kori shari'ar baki daya.