BBC Hausa of Friday, 5 March 2021

Source: BBC

An ba da tukwicin $1.5m ga masana kimiyyar da suka gano maganin ciwon kan ɓari guda

Masanan huɗu za su raba tukwicin na dala miliyan daya da rabi Masanan huɗu za su raba tukwicin na dala miliyan daya da rabi

Wasu ƙwararrun masanan kimiyya huɗu sun samu kyauta mafi daraja kan binciken da suka gudanar wajen gano asilin abin da ke haddasa ciwon kai mai tsanani na ɓari guda wato Migraine, da kuma yadda ake warkar da shi.

Masanan, waɗanda suka ƙware a ɓangaren jijiyoyin ƙwaƙwalwa sun haɗa da ɗan Birtaniya da ɗan Darmark da dan Sweden da kuma Ba'amurke, sun gano yadda hada-hadar da ke sa jijiyoyin da ke kewaye da ƙwaƙwalwa ke buɗewa har ya kai ana jin raɗaɗi.

Ƙwararrun masanan huɗu sun kuma gano yadda siddabarun ke gudana a cikin jijiyoyin da ke kewaye da ƙwaƙwalwa.

Yadda jijiyoyin ke buɗewa, tamkar kumbura, kuma buɗewar ta haddasa ciwon kai mai tsanani da ake kira Migraine.

Wannan bincike ya sa sun samar da wasu jerin magungunan da suka sarrafa domin warkar da ciwon kan mai tsanani cikin gaggawa.

Binciken ya sanar da cewa, irin wannan ciwon kai mai tsanani na faruwa ne ga mata sau uku kafin ya faru ga namiji sau daya, saboda da alaƙarsa da wani sinadari da ke da yawa ga mata fiye da ga maza a cikin jikinsu.

Wanan sinadari na hadasa ciwon kai mai tsanani da yawon tashin zuciya da juwa da kuma sa rashin son haske da kwaramniya da saka soshe-soshe.

Masanan huɗu za su raba tukwicin na dala miliyan daya da rabi daga Gidauniyar Lundbeck.