BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

An inganta rayuwar matan da ake tsangwama saboda haila a Indiya

Wasu matan Iniya a gidan su Wasu matan Iniya a gidan su

Sansanin jinin haila da ke yammacin Indiya inda ake tilasta mata da ƴan mata zuwa a lokacin da suke jinin al'ada na samu inganci.

Wata kungiyar jin-kai da ke Mumbai ta Kherwadi Socila Welfare Association na kan gudanar da aikin inganta sansanin da ke jahar Maharashtra da ke kudanci.

Yanzu haka an inganta wurin da gidaje da dakuna na zamani.

An saka gadaje da ban-daki mai kyau da ruwa mai tsabta da kuma lantarki mai amfani da hasken rana.

Amma da dama na ganin cewa a maimakon inganta wurin kamata ya yi a ci gaba da nuna adawa da wannan al'ada ta tsangwamar matan a lokacin da su ke jinin al'ada.

A ganin wasu masu adawa da al'adar yin haka tamkar nuna goyon baya ne ga wadanda suke ganin al'adar ba ta da cutarwa ga wadannan mata.

Tun asali a Indiya ana kyamar mace a lokacin da ta ke haila, kuma a kan haka ne su ke zama cikin takurawa da rashin walwala.

Kwata-kwata an haramta musu halartar duk wata hulda da al'umma ko zuwa wurin ibada ko ma shiga dakin da fa abinci.

Sai dai duk da haka irin yadda ake gudanar da al'adar a gundumar Gadricholi da ke da tsananin talauci ta yi tsauri sosai.

A duk wata masu haila a Gadricholi na sahfe kwana biyar a cikin wadannan bukkoki da ke wajen kauyukansu a gefen daji.

Ba a barinsu su dafa abinci ko su debo ruwa, suna dogara ne da dan ruwa da abinci da yan uwansu mata ke kai musu.

Kazalika idan namiji ya taba su shi ma sai ya yi gaggawar wanke jikinsa saboda ya zama ba shi da tsarki.

Amma matan kauyen Tukum da ke haila su 90 a yanzu sun ce sun samu walwala bayan da aka zamanantar musu da sansaninsu na haila.

Sun ce a baya hankalinsu kan tashi su shiga damuwa a duk lokacin da hailarsu ta kusa zuwa, ganin cewa za su je wannan wuri mai kunci.

Idan za su yi wanka ko wanki sai sun yi tafiyar kilomita guda kafin su samu rafi.

Surekha Halami mai shekaru 35 ta ce a duk lokacin zafi suna shan wahala sosai ga kuma cizon sauro.

Idan kuma sanyi ya shigo akwai sanyi sosai wanda ke hana su walwala, uwa uba idan ana ruwa kwanon da ke kan rufinsu yana tsiyaya duk zai jika inda suke kwanciya.

Wasu lokutan kwatsam sai su ga karnuka ko aladu sun fado musu.

Sheetal Narote mai shekaru 21 ta ce a duk lokacin da ta ke ita kadai a dakin, ba ta iya bacci saboda tsoro.

A cewarta ''ga duhu ciki da wajen dakin, kuma duk yadda na ke son zuwa gida ba zan iya ba saboda ba ni da zabi.''

Makwabciyarta Durpata Usendi mai shekaru 45 ta ce wata matashiya mai shekaru 21 ta taba mutuwa a wurin saboda harbin maciji.

''Wata rana mun tashi cikin dare kai sai muka ga ta fita daki a guje tana kuka tana kara.''

''Yan uwanta mata su ka kai mata agaji ta hanyar ba ta maganin gargajiya.''

''Amma 'yan uwanta maza suna ganin abin da ke faruwa daga nesa. Sai dai babu halin su taimake ta saboda tana haila.''

''Suna ji suna gani har ta mutu bayan wasu awanni.'' A cewar Duparti.

Nicola Monterio ta kungiyar KSWA ta ce sun kashe dala 8,900 wurin gina musu sansanin a cikin wata daya da rabi.

Kungiyar mai zaman kanta ta gina sansanin masu jinin haila hudu, kuma ta shirya gina karin wasu shida a wasu kauyukan da za a fara aiki da su a tsakiyar watan Yuni.

Dilip Barsagade shugaban kungiyar jinkai ta Sparsh ya ce a 'yan shekarun da suka gabata ya ziyarci sansanonin haila 223, kuma kashi 98 daga cikinsu ba su da tsabtar da ya kamata bil'adama ya zauna a cikinsu.

Binciken da Dilip ya yi ya gano cewa akalla mace 21 ce ta mutu a sansanin Kurma.

''Akwai wadda ta mutu da harbin maciji, akwai wadda wata dabba ta kashe, akwai kuma wadda ta mutu bayan fama da zazzabi mai zafi.''

Binciken Dilip ya sa kungiyar kare hakkin bil adama ta NHRC ta bukaci gwamnatin jahar da ta soke wannan al'ada saboda ta na mummunar illa da kuma matukar take hakkin mata.

Amma shekaru bayan kiran babu wani mataki da hukumomin suka dauka.

A cewar Dilip babu mace daya da ya tambaya a kauyen da ta nuna sha'awar wannan al'ada, amma saboda abu ne da suka taso suka ga ana yi shekara da shekaru ba su da zabi dole su je.

Da yawa na tsoron kauracewa zuwa sansanonin haila saboda ka da su hadu da hushin abin bautarsu.

Surekha Halami ta yi imanin cewa matsawar ta saba wa al'ada za a a samu cutuka da mace mace a danginsu.

''Kakata da mahaifiyata sun yi zama a sansanin Kurma, ni ma yanzu haka duk wata ina zuwa kuma ina fatan na tura 'yata nan gaba," a cewarta.

Chendu Usendi dattijo da ke zaune a kauyen ya fada wa BBC cewa abu ne mai wahala a iya soke al'adar, don abun bautarsu ne ya umurce su da su aiwatar da ita.

Kuma ana hukunta duk wadda ta kaurace mata ta hanyar ciyar da ilahirin kauyen naman aladu da kuma giya, ko kuma a ci tara.

To amma duk da ana jingina batun soke al'adar da addini da al'ada, har yanzu matan da ke da ilimin zamani a Indiya na ci gaba da kalubalantar wannan al'ada.

Kungiyoyin mata da dama sun garzaya kotu suna bukatar a rika ba masu haila daga cikinsu damar shiga wuraren bauta na musulmi da kirista.

Akwai ma taken #HappyToBleed da suka kirkira da ya karade shafukan sada zumunta, don nuna tirjiya kan wannan tsangwamar masu jinin al'ada a Indiya.

Kungiyar KSWA na ganin cewa wadannan mata na bukatar a taimaka musu da muhalli mai kyau kafin a samu abin da ake so na rusa al'adar a nan gaba.

Kuma wannan ya fi sauki, in ji Barsagade.

Babbar matsalar kawo yanzu, in ji shi, ita ce hatta mata ba su fahimci cewa tauye hakkinsu ne ba.