An saki sauran ɗaliban da aka sace na kwalejin Horar da Harkokin Noma da Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya da ke Kaduna.
Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban ya tabbatar wa BBC cewa an saki ɗalibai 27.
Ya ce suna kan hanyar karɓar ɗaliban.
Shiekh Ahmad Abubakar babbam malamin addinin Islama da ke da'awar yin sulhu da ƴan bindiga ya shaida wa BBC cewa su shiga tsakani tare da aka saki ɗaliban.
"Mu muka yi ƙoƙarin ganin an sake su tare da taimakon tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo," in ji Sheikh Gumi.
Sai dai bai bayyana cewa ko an biya kuɗin fansa ba kafin aka saki ɗaliban.
A watan Maris ne ƴan bindiga suka abka kwalejin gandun dajin da ke unguwar Mando a Kaduna suka saci ɗalibai 30.