Mahukuntan gasar La Liga sun sanar cewar za a buga karawar mako na 30 tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar Asabar 10 ga watan Afirilu.
Za kuma a yi karawar ta hamayya da ake mata lakabi da El Clasico tsakanin manyan kungiyoyin Spaniya a filin wasa na Alfredo Di Stefano.
Tun farko kungiyoyin sun kara a Nou Camp a gasar bana ranar 24 ga watan Oktoba, inda Real ta yi nasara da ci 3-1.
Wadanda suka ci wa Real kwallayen da ta hada maki uku a ranar sun hada da Fede Valverde da Sergio Ramos da kuma Luka Modric, inda Ansu Fati ya ci wa Barca kwallo daya.
Wasan El Clasico na biyu a bana yana da mahimmaci, watakila shi ne zai fayyace wadda za ta lashe kofin Spaniya na bana, wanda Atletico Madrid ke kan gaba a teburi.
Kawo yanzu Barcelona wadda ke mataki na biyu tana da tazarar maki hudu tsakaninta da Atletico, ita kuwa Real an bata maki shida tsakaninta da ta daya a teburin.
Real Madrid za ta ziyartar Celta Vigo ranar 20 ga watan Maris a wasan mako na 28, sannan ta karbi bakuncin Eibar ranar 3 ga watan Afirilu, sannan ta fuskanci Barcelona karawar mako na 30..
Real Sociedad za ta karbi bakuncin Barcelona wasan mako na 28 ranar 21 ga watan Maris, sannan kungiyar ta Nou Cam ta karbi bakuncin Valladolid fafatawar mako na 29 ranar 5 ga watan Afirilu, sannan ta je gidan Madrid a wasan mako na 30.