BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

An yi jana'izar matasa 13 a Ghana

An binne yara 12 cikin 13 a ranar Talata a garin Apam An binne yara 12 cikin 13 a ranar Talata a garin Apam

An binne yara 12 cikin 13 a ranar Talata a garin Apam da ke gabar teku a ƙasar Ghana.

An binne daya daga cikin matasan a ranar Alhamis saboda jikinsa ya rube sosai.

Akalla yara ashirin ne ake fargabar sun mutu amma biyu sun tsira.

Abin tayar da hankali ne da al'ummar masu kamun kifi ba su taba ganin irinsa ba. Sun shiga wani hali na dimuwa, suna mammakin yadda hakan ta faru.

Kawo yanzu wasu iyaye na zaman jiran jin labarin 'ya'yansu. An rufe rairayin bakin teku a Ghana don hana yaduwar cutar korona amma yara sun yi amfani da wata hanya don zuwa iyo.

Gabar tekun Ghana sananneN wuri ne mai hatsarin gaske saboda tsananin karfin ruwa kuma ana ba mutane shawarar yin taka-tsantsan.

Ibtila'in baya baya nan ya zama wata babbar tunatarwa ga hukumomi da su sake yin nazari a kan matakan kariya a gabar ruwan kasar.

Matasan da ake tsammanin sun kai ashirin sun fita yin ninkaya a makon da ya gabata kuma ba su dawo ba. An yi jana'izar wasu tare da fatan samun karin wasu gawarwakin nan gaba.