An yi wa wasu manyan birrai tara dake wani gandun namun daji a San Diego dake Amurka allurar rigakafin korona, bayan gano wasu birrai yan uwansu, da yawa da aka gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu da cutar.
Cikin birran har da wata mace mai suna Karen, wacce ita ce ta farko da aka fara yi wa wata tiyatar zuciya da aka yi a karon cikin shekaru talatin da suka gabata.
Daya daga cikin birran da ke dauke da cutar ta korona a gidan namun dajin akwai wani dattijo da ake kira Winston, amma a yanzu yana ci gaba da murmurewa.
Wani kamfanin hada magungunan dabbobi da ake kira Zoetis ne ya samar da rigakafin koronar, da ake yi wa dabbobi.
- Hotunan gwaggwon birran da ba kasafai a kan gansu ba 'Gwaggon biri na yada maleriya mai kisa ga mutane'