BBC Hausa of Wednesday, 24 March 2021

Source: BBC

An yi wa ‘yan Najeriya fiye da dubu 250 allurar riga-kafin korona

Ana ci gaba da yi wa 'yan Najeriya allurar riga-kafin korona Ana ci gaba da yi wa 'yan Najeriya allurar riga-kafin korona

Gwamnatin Najeriya ta ce ya zuwa yanzu an yi wa 'yan kasar fiye da 250,000 allurar riga-kafin cutar korona.

Wasu alkaluma da Hukumar Lafiya a tamakin farko ta kasar ta fitar sun nuna cewa ya zuwa ranar 23 ga watan Maris, an yi wa mutum 215,277 allurar riga-kafin korona.

Hakan na nufin kashi 5.5 cikin dari na 'yan kasar aka yi w riga-kafin.

Alkaluman sun nuna cewa jihar Lagos ce a sahun gaba a yawan wadanda aka yi wa riga-kafin, inda aka yi wa mutum 58,461, kamar dai yadda ita ce ta fi kowacce jiha yawan wadanda suka kamu da cutar korona tun bayan bullarta a Najeriyar a bara.

Idan muka je arewacin kasar kuwa, jihar Bauchi ce kan gaba, an kuma yi wa mutum 23,827 allurar riga-kafin ta AstraZeneca.

Jihar Jigawa ke biye mata da mutum 20,800.

Sauran jihohin da aka yi riga-kafin sun hada da:

    Adamawa 7,407
    Akwa Ibom 127
    Anambra 132
    Bayelsa 552
    Binuwai 146
    Borno 653
    Cross River 948
    Delta 915
    Ebonyi 77
    Edo 2,645
    Ekiti 1,049
    Enugu 956
    Abuja 8,616
    Gombe 203
    Imo 1,908
    Kaduna 14,572
    Kano 3,903
    Katsina 10,002
    Kwara 12,016
    Nasarawa 6,801
    Ogun 19,257
    Ondo 4,205
    Osun 6,658
    Filato 883
    Rivers 1,951
    Sokoto 98
    Yobe 5,509
Sai kuma jihohin da ba a yi wa ko mutum guda rigakafin cutar korona ba, sun hada da:

    Abia 0
    Zamfara 0
    Kebbi 0
    Niger 0
    Kogi 0
    Taraba 0
    Oyo 0