BBC Hausa of Saturday, 20 March 2021

Source: BBC

An zabi Finland a matsayin wuri mafi farin ciki a duniya

Rahoton ya nemi ra'ayoyin mutane a kasashe 149 Rahoton ya nemi ra'ayoyin mutane a kasashe 149

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya zabi Finland a matsayin wuri mafi farin ciki a duniya shekara hudu a jere.

Rahoton ya kuma zabi Denmark a matsayin kasa ta biyu, sai Switzerland da Iceland da Netherlands.

New Zealand ita kadai ce kasar da ba ta cikin Turai da ke jerin kasashe 10 yayin da Burtaniya kuma ta koma ta 17.

Rahoton ya nemi ra'ayoyin mutane a kasashe 149 a kan su kimanta farin cikinsu.

Rahoton ya kuma dubi sauran batutuwa da suka hada da tallafin zamantakewa, da yancin tofa albarkacin baki da arzikin cikin gida na kasa da kuma matakan da ake dauka domin yaki da cin hanci da rashawa.

Sai dai kasashen da ake ganin su ne mafi rashin farinciki a duniya sun hada da Afghanistan da Lesotho da Botswana da Rwanda da kuma Zimbabwe.

Finlanda ta yi wa sauran kasashen duniya fintikau saboda matakan da ta dauka domin karfafa aminci tsakanin al'umma wadanda sun taimaka wajan kare rayuka da ayyuka a lokacin annobar korona a cewar mawallafan rahoton.

Kasar mai yawan al'umma sama da miliyan biyar ta yi nasarar dakile yaduwar cutar idan aka kwatanta da sauran kasashen Turai, inda mutum sama da dubu 70 suka harbu da cutar yayin da 805 suka rasa rayukansu, kamar yadda alkaluman jami'ar John Hopkins suka nuna.