BBC Hausa of Tuesday, 13 April 2021

Source: BBC

Ana zaben shugaban kasa a Chadi da Jamhuriyar Benin

Masu kada kuria sama da miliyan bakwai su ka yi rajista a Chadi Masu kada kuria sama da miliyan bakwai su ka yi rajista a Chadi

Masu kada kuria sama da miliyan bakwai za su je rumfunan zabe a zaben shugaban kasar Chadi da za a yi ranar Lahadi da ake ganin zai ba Idris Deby Itno da ya shafe shekara 30 a kan karagar mulki damar samun wa'adi na shida bayan da aka hana fitattun abokan hammayarsa fafatawa da shi.

Derby shi ne dan takarar da ke gaba-gaba a zaben da yawan abokan hammayarsa ya ragu daga 16 zuwa 6 bayan da aka hanasu tsayawa takara ko suka janye.

Yayin da ya ke fuskantar 'yan takara ba tare da wani nauyin siyasa ba, Idris Derby wanda mutum ne mai karfin fada a ji a kasar kuma abokin kasashen yamma ne a yakin da ake yi da yan ta'aada a yankin sahel ga dukkan alamu zai samu wa'adi na shida a kan karagar mulki .

Sai dai jam'iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula sun shafe watanni suna zanga zanga don neman mika mulki cikin kwanciyar hankali da lumana.

Amma an hana gudanar da zanga zangar kuma an tarwatsa duk wani gangamin jama'a ta hanyar amfani da karfi, yayin da 'yan sanda da sojoji suka yi wa hedkwatar jam'iyyun siyasa da gidajen shugabanninsu kawanya.

Kungiyar kare hakkin bildama da Amnesty International da Sakatare Janarar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteresh na cikin wadanda suka yi Allah wadai da matakin amfani da karfi.

Jadawalin zabe ya nuna cewa za a sanar da sakamakon zaben na yankuna a ranar 25 ga watan Afrilu yayin da za a fitar da sakamakon karshe a ranar 15 ga watan Mayu.

A Jamhuriyar Benin kuwa 'yan takara biyu ne kawai aka ba su damar fafatawa da shugaba Patrice Tallon wadanda tsoffaffin yan majalisar dokoki ne - Allasane Soumanou da Corentin Kohoué.

Sauyen-sauyen da aka yi wa tsarin zaben kasar sun hana dukkanin fitattun 'yan hammaya na kasar Benin tsayawa takara ko suna gudun hijira sakamakon barazanar hukuncin dauri mai tsanani a gidan kaso.

Mr Talon wanda a baya ya sha alwashin yin wa'adi guda kawai shi ne ake ganin zai yi nasarar samun karin shekara biyar a kan karagar mulki.