BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Anya Ronaldo zai ci gaba da wasa a Juventus kuwa?

Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo, dan kwallon Juventus

Ranar Lahadi AC Milan ta je ta doke Juventus da ci 3-0 a gasar Serie A da suka buga, hakan ya kara sa Juve cikin matsi a wasannin da suka rage mata.

A karawar ta ranar Lahadi Cristiano Ronaldo ya kasa taka rawar da ta dace, hakan ya sa wasu magoya baya suke sukar kwazon da yake yi a wasanninsa.

Rashin nasarar da Juventus ta yi a gasar ta Italiya ya kai ta mataki na biyar a teburin da maki 69, bayan da tuni Inter Milan ta lashe kofin bana.

Hakan ne ya kawo karshen kaka tara da Juventus tana lashe Serie A a jere, inda Inter ta ci na farko tun bayan shekara 11.

Ronaldo bai nuna kansa a karawa da Milan ba, bai buga kwallon da ta nufi mai tsaron raga Gianluigi Donnarumma ba, kwallo biyu ya kai hari duk suka yi fadi.

Tun a baya wasu na tamabayar makomar kyaftin din Portugal, wanda yanzu alamu na nuna cewar da kyar ne idan zai ci gaba da taka leda a Italiya.

Ronaldo yana da kwantiragi da zai kare a karshen Yunin 2022, amma wasu rahotanni na cewar watakila ya koma Manchester United da buga Premier League.

Wasu rahotannin na cewar watakila ya koma tsohuwar kungiyarsa Sporting CP, domin ya karkare sana'arsa ta tamaula a Portugal.

Inter Milan ce ta daya a kan teburi da maki 85 wadda ta lashe kofin bana, sai Atalanata ta biyu mai maki 72, iri daya da wanda AC Milan take da shi.

Kungiyar Napoli ce ta hudu a teburi mai maki 70, sai Juventus ta biyar da maki 69, kuma sauwa wasa uku-uku a karkare kakar bana.

Wadan da ke kan gaba a cin kwallaye a Italiya:

  1. Cristiano RonaldoJuventus 27


  2. Luis Muriel Atalanta 21


  3. Dusan Vlahovic Fiorentina 21


  4. Romelu Lukaku Inter Milan 21


  5. Simeon Nwankwo Crotone19


  6. Ciro Immobile Lazio 19


  7. Lorenzo Insigne Napoli 17


  8. Domenico Berardi Sassuolo 16


  9. Lautaro Martinez Inter Milan 16


  10. Joao Pedro Galvao Cagliari Calcio 16


  11. Zlatan Ibrahimovic AC Milan 15