BBC Hausa of Friday, 12 March 2021
Source: BBC
Dan wasan Inter Milan, Arturo Vidal zai yi jinya, bayan da likitoci za su yi masa aiki a gwiwar kafarsa ranar Juma'a, kamar yadda kungiyar ta sanar.
Za a yi wa dan kwallon Chile aikin ne a wata cibiyar lafiya da ke Kudancin Milan, kamar yadda kungiyar ta bayyana ranar Alhamis.
Vidal mai shekara 33 ya ci karo da koma bayan raunin da yake yawan jinya a kakar bana da hakan kan hana shi buga wasanni da yawa.
Inter za ta ziyarci Torino wadda ke ta ukun karshe a teburi domin buga gasar Serie A ranar Lahadi, bayan da kungiyar ke fatan cin wasa na takwas a lik a jere.
Inter Milan na fatan lashe kofin Serie A na bana, kuma a karon farko tun bayan shekara 11 rabon da ta lashe shi.
Kungiyar tana ta daya a kan teburi da maki shida tsakaninta da abokiyar hamayya Milan.