BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Asalin Ranar Mata Ta Duniya da dalilin da ya sa ake bikinta

Kowani shekara Maris 8 ne Ranar Mata Ta Duniya Kowani shekara Maris 8 ne Ranar Mata Ta Duniya

Me yiwuwa kun taba ganin bubukuwan Ranar Mata ta Duniya a kafafen yada labarai, ko kuma jin abokai na magana game da ita.

Amma game da menene? Wane lokaci ne? Bukukuwa ne ko kuma zanga-zanga? Shin akwai Ranar Maza ta Duniya ne kamar irin wannan? Kana wadanne muhimman bukukuwa ne za a gudanar a cikin wannan shekarar?

Fiye da karni guda mutane a fadin duniya na gudanar da bukukuwa a ranar 8 ga watan Maris a matsayin ranar mata ta musamman.

Karanta don ka gano dalilin da ya sa.

1. Mene ne asalin fara ta?

Ranar Mata ta Duniya, ta samo asali ne daga kungiyar kwadago don neman ta kasance cikin ranakun da majalisar Dinkin Duniya ta san da su a ko wace shekara.

An kuma kafa ta a shekarar 1908, lokacin da mata 15,000 suka gaudanar da gangami a fadin birnin New York suna neman a rage musu yawaan lokutan aiki, da albashi mai kyau, da kuma ba su 'yancin kada kuri'a.

Shekara guda bayan haka ne jam'iyar Socialist ta Amurka ce ta ayyana Ranar Mata ta Duniya ta farko.

Shawarar mayar da ranar ta kasance ta duniya baki daya ta samo ne daga wata mata mai suna Clara Zetkin.

Ta bullo da shawarar ne a shekarar 1910 a wani babban taron kasa da kasa kan mata a birnin Copenhagen.

Mata 100 ne suka halarci taron daa kasashe 17, kuma suka amince da shawararta nan take.

An fara gudanar da bikin ne a shekarar 1911, a kasashen Austria, da Germany da kuma Switzerland.

An kuma gudanar da bikin cike shekaru 100 da bullo da bikin ranar a shekarar 2011, don haka a cikin wannan shekarar za mu yi bikin cika shekaru 110 na fara bukin Ranar Mata da Duniya.

A shekarar 1975 ne aka tabbatar da bikin ranar a hukumance, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta fara bikin wannan rana.

Taken bikin na fako da Majalisar Dinkin Duniyar ta tsayar a shekarar 1996 shi ne "Bikin tuna baya, tsara rayuwa ta gaba''.

Ranar Mata ta Duniya ta zama ranar bikin duba halin da mata ke cikin a tsakanin al'umma, a fannonin siyasa, da tattalin arziki, yayin da a tushen siyasar hakan na nufin yajin aiki, kuma a kan shirya gudanar da gangami don fadakarwa game da cigaba da nuna wariya

2. Yaushe na Ranar Mata ta Duniya?

Ranar 8 ga watan Maris ne. Ranar Mata ta Duniya da Clara ta bullo da shawara a kai ba ta da takamaimen rana da aka tsayar.

Ba ta kasance a hukumance ba har sai a lokacin wata zanga-zangar lokacin yaki a shekarar 1917 lokacin da matan kasar Russia suka bukaci ''biredi da zaman lafiya'' - kana kwanaki hudu da fara yajin aikin matan, aka tilasta wa shugaban ya sauka daga mukaminsa kana gwamnati ta amince wa mata samun 'yancin kada kuri'a.

Ranar Lahadi 23 ga watan Fabrairu ne da matan suka fara gudanar da yajin aikin kan tsarin kalandar kwanan wata ta Julian da kasar Russia ke amfani da ita a wancan lokacin.

A yanzu wannan rana a kan tsarin kalandar Gregorian ne ta kasance ranar 8 ga watan Maris- shi yasa a yau ake wannan a yau.

3. Wadanne launuka ne a alamun Ranar Mata ta Duniya?

Algashi, da, kore, da kuma su ne launukn Ranar Mata ta Duniya.

"Launin algashi yana nuna alamar adalci da mutuntaka. Kore kuma na nuna alamun fata nagari. Fari kuma na nuna tsakaka.

Launukan sun samo asali ne daga kungiyar kyautata jin dadi da harkokin siyasar mata (WSPU) a kasar Birtaniya a shekarar 1908," in ji gangamin na Ranar Mata ta Duniya.

4. Shin akwai Ranar Maza ta Duniya kuwa?

Sosai ma kuwa akwai, ranar 19 ga watan Nuwamba.

Amma an kawai gudanar da bikin ranar ne tun a shekarar 1990, kuma Majalisar Dinkin Duniya ba ta san da ita ba.

Mutane sun yi bikin ranar a fiye da kasashe 80 da suka hada da Birtaniya.

Ranar na biki tunawa da '' abubuwan alkhairin da maza suka bayar da gudumawa a akai ga duniya, da iyalansu, da kuma al'ummarsu'', tare da nuna maza abin koyi da kuma fadakarwa game da kyutata jin dain mazan.

Taken bikin na shekarar 2020 shi ne "Ingantacciyar kiwon lafiya ga maza da 'yaya maza''.

5. Yaya ake gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya, kuma akwai bukukwan ma a cikin wannan shekarar?

Ranar Mata da Duniya ranar hutu ce a kasashe da dama da suka hada da Russia inda ake kara yawan yadda aka saba sayar da furanni a cikin kwanaki uku zuwa hudu daf da 8 ga watan Maris.

A kasar China, ana bai wa mata da dama hutun rabin ranar a wuraren ayyukansu a ranar 8 ga watan Maris, kamar yadda gwamnati ta bayar da umarni, duk da cewa wasu shugabannin ma'aikatun ba su cika bai wa mata ma'ikatan wannan dama ba.

A kasar Italiya, ana gudanar da Ranar Mata ta Duniya, ko kuma 'la Festa della Donna,' ta hanyar raba furanni masu launin rawaya.

Babu tabbacin dalilin daukar irin wannan al'ada, amma kuma an yi amanna ta samo asali ne daga birnin Rome bayan yakin duniya na biyu.

A Amurka, watan Maris wata ne mai muhimmanci gtarihin mata.

A kan fitar da sanarwa a ko wace shekara da ke dauke da batutuwa na girmama mata Amurkawa da irin cigaban da suka samu.

Wannan shekara za ta kasance da banbanci saboda annobar cutar korona da kuma cewa akwai wasu taruka da za su faru a fadin duniya a daidai wannan lokaci.

6. Menene taken bikin Ranar Mata ta Duniya na shekarar 2021?

An zabi taken gangamin bikin Ranar Mata ta Duniya na wannan shekarar ya kasance #ChooseToChallenge da nufin cewa duniyar mai cike da kalubale, duniya ce mai saurin ankara, duka muna da nauyin da ya rataya a wuyanmu kan tunani da kuma daukar mataka.

"Za kuma mu iya zabar kalubalantar mu yi kira ga nuna wariyar jinsi,'' kasashe masu gangami." Za kuma mu iya zabar neman gudanar da bikin murnar tunawa da cigaban da mata suka samu."

7. Me yasa muke bukatarta?

Haka kuma, bayanan da aka tattara a baya bayan nan daga ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai lura da harkokin mata ya nuna cewa annobar cutar korona ka iya kawar da duka matsalar nuna wariyar jinsi na shakara 25.

Akasari mata sun fi gudanar da ayyukan cikin gida da kula daiyali saboda annobar wanda daga baya ka iya yin mummunan tasiri wajen samun damar karatu da kuma ayyukan yi.

Duk da damuwar da ake da ita game da annobar cutar korona, an gudanar da gangamin Ranar Mata ta Duniya ta shekarar 2020.

Yayin da akasari an gudanar cikin lumana, a Bishkek babban birnin kasar Kyrgyztan, 'yansanda sun tsare gwamman mata masu fafutikar kare hakkin mata jim kadan bayan da aka bayar da rahoton cewa wasu mutane rufe da fuskoki suka kai farmaki kan taron masu gangamin.

Masu fafutikar sun ce al'amuran da suka shafi hakkin mata na kara tabarbarewa a kasar.

A fadin kasar Pakistan, an gudanar da gangamin a birane da dama duk da baraana da kuma kararrakin da aka gabatar.

Kana a kasar Mexico mutane kusan 80,000 ne suka bazu a kan titina don nuna yadda ake cin zarafin mata a kasar, amma kuma hakan ya haifar da jikkatar mutane fiye da 60.

Duk da cewa an fara gudanar da gangamin cikin lumana, 'yasanda sun ce mutanen sun rika jifan jami'an 'yansandan da ababan fashewar da aka hada da man fetur, da ya sa jami'an suka mayar da martani da hayaki mai saka kwalla.

A cikin shekaru kadan da suka gabata, mun ga cigaban da aka samu, kana kungiyoyin mata sun kai matsayi na ba-zata.

A cikin wannan shekarar kuma an rantsar da Kamala Harris a matsayin mace bakar fata kuma 'yar yankin Asia Ba Amurkiya ta farko a matsayin mataimakiyar shugaban Amurka.

A shekarar 2019, kasar Finland ta zabi sabuwar gwamnatin karkashin jagorancin mata biyar, an soke dokar hana zubar da ciki a Northern Ireland da kuma kawar da dokar da ke yiwa mata iyaka game da irin shigar kayan da mata ya kamata su yi a bainar jama'a a kasar Sudan.

Menene mata 100?

BBC 100 Women ko kuma shirin BBC na mata 100 na duba matan da suka yo zarra tare da karfafa gwiwar mata a fadin duniya a ko wace shekara. Mu kan tsara rahotannin na musamman, da tarihi, da hirarraki, tare da bayar da isasshiyar dama ga rahotannin da kan fito da matan.

Ku biyo shirin na BBC 100 Women a shafinmu na Instagram da Facebook domin shiga cikin tattaunawar.