BBC Hausa of Friday, 5 March 2021

Source: BBC

Atletico da Real za su fafata karo na 30 a kaka takwas

Atletico da Real Atletico da Real

Ranar Lahadi ne Real Madrid za ta ziyarci Atletico Madrid, domin buga wasan hamayya a gasar La Liga fafatawar mako na 26.

Kungiyoyin biyu sun fuskanci juna fiye da sauran masu buga La Liga tun daga kakar 2013/14, kuma wasa na 30 da za su kece raini a tsakaninsu.

A karawar farko a La Liga da za su fafata a bana ranar 12 ga watan Disamba, Real ce ta yi nasara a gida da ci 2-0.

    Madrid ta kara tazara a saman teburin La Liga Real Madrid ta haye teburin La Liga
Atletico ce ke jan ragamar teburin La Liga na bana da maki 58 da kwantan wasa daya, Real Madrid mai maki 53 tana ta uku a teburin na gasar Spaniya.

Cikin wasa 29 da suka kara tun daga 2013/14 sun hadu a La Liga sau 15 da karawa a Champions League karawa shida.

Sauran fafatawar sun kara a Copa del Rey karo hudu da wasa uku a Spanish Super Cup da gumurzu daya a European Super Cup.

Tun daga wasan European Super Cup a Agustan 2018, Real ta yi nasara a wasannin hamayya shida, kuma ba a doke ta ba.

Ciki har da wanda Real Madrid ta lashe Spanish Super Cup a Jeddah a Janairun 2020, bayan da ta yi nasara a kan Atletico a bugun daga kai sai mai tsaron raga.