Tun bayan da makamai masu linzami suka fara sauka a kusa da gidansu a yankin Zirin Gaza cikin wannan makon, Najwa Sheikh-Ahmad ta kasance cikin fargabar yin barci.
"Dare ya kasance abin fargaba a gare mu - ga 'yayanmu,'' Najwa, wata uwa mai 'ya'ya biyar ta bayyana. "Cikin lokaci kankane gidanka zai iya zama kabarinka."
A duk tsawon rana, tana jin rugugin jiragen yakin kasar Isra'ila ta sama, tare da karar fashewar makamai masu linzami da kuma luguden wuta ta sama. "Komai yana girgiza a kusa da mu," in ji ta. "Kana mu kanmu ma karkarwa muke yi saboda muna cikin razana."
Tana daga cikin mazauna Isra'ila da Gaza da dama da suka fada cikin fargaba, yayin da dakarun Isra'ila da mayakan Falasdinawa ke ci gaba da musayar wuta, ga kuma arangamar kan tituna da ta barke tsakanin Yahudawa da Larabawan Isra'ila a garuruwan Israi'la da dama.
Mutane akalla 83 ne aka hallaka a Gaza kana bakwai a Isra'ila.
BBC ta tattauna da wasu iyaye mata - daya Bafalasdiniya, daya kuma Bayahudiyar Isra'ila - wadanda mummunan rikicin ya rutsa da su a yankin da ya sha fama a cikin shekaru da dama.
'Boye fargabarka ba abu ne mai sauki ba'
Yayin da daruruwan makamai masu linzamin Isra'ila suka fada kan Gaza a ranar Laraba da dare, iyalan Najwa Sheikh-Ahmad sun hadu wuri guda a tsakiyar hawa na daya na benen gidansu.
Fargabar cewa bam ka iya fadawa kan gidansu ya zama abun tsoron da ba zai iya misaltuwa ba, in ji Najwa.
"Cikin dakikoki kadan za ka iya jin luguden wuta a kusa da kai, a kan gidanka ko a kan na makwabcinka," ta ce. "Wannan ka iya sauya wurin da ya kamata a ce gidan ka ne zuwa kabarin ka kai da 'yayanka, da burin ka, da komai naka."
Najwa na zaune tare da mijinta da 'ya'yansu biyar, daga shekaru 11 zuwa 22, a kusa da sansanin 'yan gudun hijira a tsakiyar yankin Zirin Gaza - wani karamin wuri cike da jama'a a kusa da tekun Bahar Rum inda mutane miliyan daya da dubu dari takwas ke zaune.
Gwamman fararen hula, da suka hada da kananan yara 17 na cikin wadanda suka hallaka a hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a kan kungiyar Hamas masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama, kamar yadda hukumomi a Gaza suka bayyana.
Isra'ila ta ce gwamman mutane da suka mutu a Gaza mayakan na Hamas ne, kuma wasu mace-macen sun faru ne saboda kuskuren harba makaman roka daga Gaza.
Fargabar da Najwa ke yi ta karu ne saboda maganganun da ake yi cewa akwai yiwuwar Isra'ila ta fara kai hare-hare ta kasa a Gaza.
"Ba za ka samu kwanciyar hankali na," a cewarta. "A matsayina na uwa akwai ban tsoro, akwai galabaita a cikin rai na da kuma tausayawa."
Najwa na wasu-wasin fada wa 'yayanta game da tashin hankalin da ke shirin faruwa a kusa da su.
Ta ce: "Na daina fada musu komai". "(Amma) boye fargabarka ba abu ne mai sauki ba.
"Saboda ba ka san ko wurin ya dace da kwanciyar hankali ba ko akasin haka."
Amma duk da kokarin ta na kauce-kaucen da ta ke yi wa 'yayan ta daga maganar yakin, Najwa ta san ba zai yiwu ta kaucewa hakan ba.
"Suna bin diddigin labarai a ko wace rana, ko da kuwa na ce kada su yi," in ji ta. "Akwai a ko ina a shafukan Instagram da na sada zumunta. Duka lalata komai ne."
Najwa ta damu game da yadda maimacin tashin hankalin da ke faruwa a Gaza a baya-bayan nan ke shafar 'yayanta.
Karamin dan ta Mohammed, wanda ya kusa cika shekara 12 har ya riga ya san tashin hankalin yake-yaken Isra'ila da Gaza na shekarar 2008 zuwa 2009 da kuma na shekarar 2014, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubbab fararen hula.
"Ina tunanin yadda idan ya girma - wadanne irin abubuwa ne zai so ya bayyana wa 'yayansa?"
Yayin da hare-hare ta sama ya kara ta'azzara, Najwa na tunanin mummunan tasirin da yake yi wa ita kan ta.
"Ba za ka taba iya sabawa da fargaba ba, ba za ka taba sabawa da jin kuka da ihun yar aba," ta ce.
'Muna tsananin fargabar cigaba da zama'
Lokacin da gungun Larabawan-Isra'ila suka isa kan titin wajen gidan su a garin Lod ranar Litinin da dare, Tova Levy ta fahimci cewa lokaci ya yi da iyalnta Yahudawan-Israi'la sun tsere.
A iya tsawon yammacin, Tova na ta karanta labaran abubuwa marasa dadi da ke cigaba da faruwa ta dandalin sada zumunta na manahajarta ta WhatsApp. Abokai sun aike da sakonnin gargadi cewa "gungun mutane" sun bar wasu masallatan yankin, kuma sun sun fara hargitsi a fadin garuruwan Isra'ila, da ke da hadin gambizar Larabawan-Isra'ila, da ke da nisan kilomita 15 (mil9) kudu maso gabashin garin Tel Aviv.
Ba da jimawa ba, ta ce, masu hargitsin suka iso kusa da gidansu, inda suke zaune tare da mijinta da 'yayan su kananan biyu.
"Sun fara kone-kone. Abin da ban tasoro… na tsorata,'' Tova ta bayyana. "Na yi tunanin, ' ko me ya hana su isowa nan su balle kofar gidana?'"
Nan da nan iyalan suka kwashe wasu daga cikin kayansu suka tsere kudanci, gidan danuwan mijin Tova, a kusa da Beersheba. "Mun tsere saboda muna cikin fargabar cigaba da zama,'' ta ce.
Tun bayan da suka fice, rikicin kan titin a garin Lod ya kara kazanta. Zanga-zangar Larabawan-Isra'ila a garin ta juye ta zama mummunan tashin hankali a ranar Talata da dare.
Masu zanga-zangar sun yi arangama da 'yan sanda inda suka banka wa motoci da gine-gine wuta, kwana daya bayan jana'izar wani mutum da aka yi zargi wasu Yahudawa sun hallaka.
Magajin-garin ya ayyana: "Yakin basasa ya barke a garin Lod."
Tova ta umarci makwabcinta da ya dauki has mezuzah, wani kyalle mai dauke da rubutun wata addu'a a jiki, wanda iyalan Yahudawa da dama ke makalawa a bakin kofar gidajen su a matsayin tunatarwa cewa Allah na nan.
"Na cika da fargabar cewa gungun mutanen za su iya abkawa cikin gidanmu,'' ta ce.
Tova ta damu game da abinda zai yi saura idan suka koma.
"Ba mu sani ba ko za mu sake samun gidan da zamu sake zama idan muka koma. Ban sani ba ko za mu tarar an tarwatsa gidanmu idan muka koma.''
Tun bayan da iyalan Tova suka bar Lod, garin ya ci gaba da fuskantar harin makaman roka.
Larabawan-Isra'ila biyu ne suka hallaka a lokacin da aka harba makaman rokar a kan motar su daga Gaza a ranar Laraba.
Yayin da ake ta jin jiniyar hari ta sama a tsawon daren, dubban mutane ne suka nemi mafaka da suka hada da Yahudawa makwabtan Tova da dama da suka rage a garin Lod.
Sun hadu wurin guda da makwabtan su Larabawa, da suka yi amanna akwai yiwuar suna cikin wadanda suka shiga zanga-zangar, da hakan ya sa suka kara tsorata.
"Wasu sauran iyalan sun yanke shawarar kada su shiga cikin maboyar karkashin kasa," a cewarta. "Wasun su kuma sun sauka kasa kadan iya yadda suka za su iya kai wa."
Yayin da wutar rikicin ta kara ruruwa, Tova tana wasu-wasin bayyana wa karamin dan ta mai shakaru hudu da rabi.
"Ya san cewa akwai tashin bama-bamai saboda mutanen da ba su da kirki,''a cewarta. "Har yanzu ina jin kamar b azan iya fada masa cewa Larabawa ne ke aikata mana wannan ba. "Ina son ya zauna cikin kwanciyar hankali a cikin makwabtan shi. Ba na son ya girma da tsoron Larabawa."
Tova ta damu cewa iyalanta za su ci gaba da samun kansu cikin mummunan tashin hankali.
"Mu fararen hula ne kuma muna fada da juna," ta ce. ''Akwai ban tsoro; akwai matukar ban tsoro, sosai da sosai."