BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Ba za mu iya biyan mafi kankantar albashi ba - Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ba za ta iya biyan mafi kankantar albashi na kasa ba, wato naira 30,000.

Gwamnatin ta ce duba da halin matsin tattalin arziki da ake ciki zai yi matukar wuya ta iya biyan albashin na watan Maris wanda daman matakin wucin gadi ne aka dauka.

Kwamishin yada labarai, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya aikewa manema labarai, ya kara da cewa raguwar kasafin da gwamnatin tarayya ke bai wa jihohi shi ya janyo hakan, wanda zai yi wuya gwamnatin Kano ta iya fara biyan sabon albashin.

Malam Garba ya ce a watan Maris da ya wuce gwamnatin jihar Kano ta karbi tallafin kasafin Naira biliyan 12, 400, 000, 000 daga gwamnatin tarayya, wanda Naira biliyan 6, 100, 000, 000, 000 shi ne na ta, ya yin da kananan hukumomi 44 da ake da su a jihar suka dauki Naira biliyan 6, 300, 000, 000.

Kwamishinan ya kara da cewa idan har gwammanati na son biyan mafi kankantar albashi ga ma'aikata, to ta na bukatar karin biliyoyin naira wanda a halin yanzu babu sukunin yin hakan.

Sanarwar ta kara da cewa lokacin da shugabannin 'yan kwadago suka tattaunawa da gwamnati a watan Mayun bara, sun fahimci cewa biyan ma'aikata sabon albashin, ya danganta ne ga abin da gwamnati ta samu na kasafin kudi.

Malam Garba ya ce idan an tuna a watan Nuwamba da Disambar bara, an dauki kwatankwacin irin wannan matakin na wucin gadi, lokacin biyan albashin ma'aikatan sakamakon rashin samun isassun kudaden shiga ga gwamnati.

Amma gwamnati ta biya ma'aikata cikakken albashi a watan Junairu da Fabrairu lokacin da abubuwa suka inganta.

Sanarwar ta ce idan ba a manta ba, jihar Kano ta na daga cikin jihohin Najeriya na farko da suka fara amincewa da biyan mafi kankantar albashi ba tare da bata lokaci ba, wanda ya kamata ace kungiyar kwadago ta yi la'akkari da shi.

Ka mata ya yi ace sun yi duba da hadin kan da gwamnatin jihar Kano ta yi tun da fari, su yi mata uzuri saboda tsunduma yajin aiki a wannan lokaci ba shi ne zai magance matsalar ba.

A karshe sanarwar ta ce gwamnatin jiahr Kano na da kyakkyawar alaka da kungiyar kwadago da ma'aikata a jihar, kuma ta tabbatarwa da ma'aikatan cewa za a ci gaba da biyansu albashin da zarar lamura sun daidaita.