BBC Hausa of Wednesday, 10 March 2021

Source: BBC

Ba zan karbi aikin kocin tawagar Jamus ba - Jurgen Kloop

Kocin Liverpool Jurgen Klopp Kocin Liverpool Jurgen Klopp

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba zai karbi aikin horar da tawagar Jamus ba, domin maye gurbin Joachim Low.

Hukumar kwallon kafar Jamus ce ta sanar da cewar Low zai ajiye aikin, idan an kammala gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2021.

Klopp ya ce ba zai zama kocin tawagar Jamus ba, bayan karkare gasar nahiyar Turai, ''akwai masu horarwa 'yan kasar Jamus da yawa kamata ya yi a bai wa wani aikin''.

Klopp mai shekara 53, ya karbi jan ragamar Liverpool a Oktoban 2015 ya kuma lashe Champions League a 2019 da Premier League a 2019-20.

Kofin na Premier shi ne na farko da Liverpool ta lashe a bara da tazarar maki 18 tun bayan shekara 30, amma a bana tana fama da kalubale.

Liverpool wadda 'yan wasanta da dama suke jinya ta yi rashin nasara a wasa shida a jere a Premier League a bana tana ta takwas a kan teburi.

Klopp ya ce zai kammala kaka uku ta yarjejeniyarsa a Liverpool da ta rage masa kamar yadda ya yi a Mainz da kuma Borussia Dortmund.

Kocin ya yi wadan nan kalaman kafin wasan da Liverpool za ta yi da RB Leipzig a Champions League ranar Laraba.

Liverpool ce ta yi nasara a wasan farko da ci 2-0, za su kara fafatawa karo na biyu a Budapest a dai gasar ta zakarun Turai.