BBC Hausa of Saturday, 1 May 2021

Source: BBC

Barcelona ta ga ta leko ta koma a gasar La Liga

Lionel Messi, dan wasan Barcelona Lionel Messi, dan wasan Barcelona

Barcelona ta barar da damar hawa kan teburin La Liga, bayan da Granada ta doke ta da ci 2-1 a Camp Nou ranar Alhamis.

Kyaftin Lionel Messi ne ya fara zura kwallo a raga, bayan da ya yi bani in baka da shi da Antoine Griezman.

Barcelona ta barar da damar makin kara zura kwallo a raga, daga baya Darwin Machis ya farke wa Granada a karawar zagaye na biyu, bayan da suka yi hutu.

Saura minti 11 a tashi daga wasan ne Jorge Molina wanda ya shiga fafatawar daga baya ya kara na biyu da hakan ya bai wa Granada maki ukun da take bukata.

Da kungiyar ta Camp Nou ta ci wannan karawar da tuni ta hau kan teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Atletico Madrid mai maki 73.

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta uku da maki 71 iri daya da na Real Madrid wadda take ta biyu a teburin da Atletico ke jan ragama.

Kawo yanzu sauwa wasa biyar-biyar a karkare kakar La Liga ta bana.

Ranar 8 ga watan Mayu za a fafata tsakanin Barcelona da Atletico Madrid a karawar da ake hangen kila a tantance wadda za ta lashe La Liga na bana a ranar.