BBC Hausa of Friday, 12 February 2021

Source: BBC

Barcelona ta yi wasa ba ta ci kwallo ba a karon farko tun Disamba

kwallo kwallo

Ranar Talata Barcelona ta sha kashi a hannun Sevilla da ci 2-0 a gidan Sevilla a wasan daf da karshe zagayen farko a Copa del Rey.

Minti 25 da fara wasa Jules Kounde ya fara ci wa Sevilla kwallo, sannan tsohon dan wasan Barcelona, Ivan Rakitic ya kara na biyu.

Rabon Barcelona kamfar cin kwallo tun karawar da Juventus ta doke ta ranar 8 ga watan Disamba a Camp Nou a Champions League.

Tun daga lokacin tana cin kwallo akalla daya ko fiye da haka a dun karawar da ta yi.

Tun bayan da Barcelona ta sha kashi a hannun Juventus ta yi wasa 16, wadda kan zura kwallo a kowanne.

Cikin karawar da ta yi har da a gasar LaLiga da Champions League da Copa del Rey da kuma Supercopa de Espana.

    Fitattun ‘yan wasan kwallon kafa da kwantiraginsu zai kare a bana Pochettino ya yi magana kan makomar Messi, Man City na son Haaland
Barcelona za ta karbi bakuncin wasa na biyu na daf da karshe a Copa del Rey ranar 3 ga watan Maris.

Barcelona wadda aka doke a wasan karshe a Spanish Super Cup za ta buga Champions League da Paris St Germain cikin watan Fabrairu.

Sannan kungiyar wadda ba ta ci kofi ba a bara tana ta uku a kan teburin La Liga na bana.