BBC Hausa of Tuesday, 13 April 2021

Source: BBC

Barcelona ta zama kungiyar tamaula mafi arziki a duniya

Barcelona ta doke Real Madrid a matakin kungiyar kwallon kafa da take kan gaba a arziki a fadin duniya.

Mujallar kididdigar kudi ta Forbes ce ta bayyana hakan ranar Litinin, inda ta ce kungiyar ta Camp Nou tana da dalar Amurka bilyan 4.76.

Real Madrid wadda ta rike mataki na daya karo biyar a baya ta koma ta biyu mai dalar Amurka biliyan 4.75.

Forbes ta ce matsakaicin kudin shiga da kungiyoyi 20 suka samu a kaka biyu ya karu zuwa kaso 30 cikin 100 wato dalar Amurka biliyan 2.28.

Kungiyoyin sun samu wannan arikin duk da kalubalen da cutar korona ta haddasa da ta kai ba sa samun kudin shiga kallon wasa ido da ido a kowanne mako.

Rashin shiga stadiya sakamakon tsoron yada cutar korona ya sa kungiyoyin sun yi hasarar dalar Amurka miliyan 441 a kakar bara wato kaso 9.6 cikin dari tun daga 2017/18.

Mai rike da kofin Champions League wato Bayern Munich, ita ce ta uku a arziki a duniya mai dalar Amurka biliyan 4.215.

Kungiyoyin Premier League shida wato Manchester United da Liverpool da Manchester City da Chelsea da Arsenal da kuma Tottenham suna cikin goman farko.

Mai rike da kofin gasar Faransa wato Paris St Germain tana ta tara da dalar Amurka biliyan 2.5 wato karin kaso 129 cikin 100 da ta samu cikin shekara biyu.

PSG ita ce wadda ta samu karin kudi da yawa daga cikin goman farko a jerin kungiyoyin kwallon kafa da suka fi arziki a duniya kamar yadda Forbes ta wallafa.