BBC Hausa of Wednesday, 19 May 2021

Source: BBC

Benzema ne gwarzon dan kwallon Faransa da ke wasa a waje

Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid ta tawaggar Faransa Karim Benzema, dan kwallon Real Madrid ta tawaggar Faransa

An bayyana dan wasan Real Madrid, Karim Benzema a matakin gwarzon dan kwallon Faransa da ke taka leda a waje a kakar bana.

Kungiyar kwararrun 'yan kwallon Faransa ce ta bayyana Benzema a matakin wanda ba kamarsa a kakar tamaula ta 2020/21 da ke taka leda a waje.

Cikin wadan da ya yi takara da su sun hada da Hugo Lloris da N'Golo Kante da Paul Pogba da Ousmane Dembele da Ferland Mendy da sauran su.

Wannan ne karo na biyu da Benzema ya lashe kyautar bayan 2019, duk da cewar Didier Deschamps baya gayyatarsa tawagar kwallon kafar Faransa.

Benzema ya ci wa Real Madrid kwallo 29 a kakar nan, kungiyar da take sa ran lashe La Liga na bana, bayan da take mataki na biyu a teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Atletico mai jan ragama.

Wannan kyautar da Benzema ya lashe ta zo ne kwana daya tsakani da ake sa ran Deschamps zai bayya 'yan wasan da za su wakilci Faransa a gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.

Tun a bara ya kamata a buga gasar cin kofin nahiyar Turai, amma cutar korona ta kai tsaiko da aka dage fafatawar zuwa 2021.