Real Madrid da Atletico Madrid sun tashi 1-1 a wasan La Liga karawar mako na 26 da suka fafata ranar Lahadi.
Luis Suarez ne ya fara cin kwallo minti 15 da fara wasa a filin Alfred Di Stefano.
Wannan ne kwallon farko da Suraez ya ci wa kungiyar tun bayan da ya yi wa Atletco wasa biyar bai zura kwallo a raga ba.
Kwallon da Suarez ya ci Real shi ne na 12 a karawar da ya fuskance ta, kuma na farko a Atletico, sauran 11 a Barcelona ya ci su.
Karim Benzema ne ya farke kwallon saura minti biyu a tashi daga karawar ta hamayya.
Da wannan sakamakon Atletico mai kwantan wasa daya ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 59.
Barcelona ce ta biyu da maki 56, bayan da ta je ta doke Osasuna 2-0 ranar Asabar.
Real Madrid ita ce ta uku da maki 54, bayan buga karawa 26 a kakar bana a La Liga.
Ranar Laraba wato 10 ga watan Maris, Atletico za ta karbi bakuncin Atletico Bilbao, domin buga kwantan wasa.