Yayin da al'ummar Musulmi a fadin duniya ke shirin bikin Karamar Sallah, rahotanni daga Najeriya na cewa kudin sufuri ya karu, yayin da wasu 'yan kasar suka fara bulaguro zuwa jihohinsu na ainihi don yin shagulgulan bikin.
Dama dai ba sabon abu ba nee karin farashin kudin mota a lokaci irin wannan da jama'a ke tafiya garuruwansu.
Wasu fasinjoji da BBC ta zanta da su sun bayyana takaicinsu game da ƙarin kudin motar, sai dai kungiyoyin sufurin na cewa dole ce ta sanya su daukar wannan mataki, saboda da yanayin da ake ciki
Duk lokaci na bukukuwa kamar Karamar Sallah ko Babba ko ma bikin Kirsimeti da na Ista a kan samu tashin kudin mota a Najeriya, saboda yadda jama'a ke yin tafiye tafiye don ziyartar 'yan uwansu.
Saurari rahoton Abdou Halilou