Bill da Melinda Gates sun sanar da mutuwar aurensu bayan shekaru 27 suna tare, suna mai cewa "mun fahimci ba za mu iya ci gaba da rayuwa tare a matsayin ma'aurata ba".
"Bayan nazari mai zurfi da ƙoƙarin daidaita zaman mu, mun yanke shawarar kawo karshen aurenmu," a cewar sakon da mutanen biyu suka wallafa a shafin Tuwita.
Sun soma haduwa a shekarun 1980 lokacin da Melinda ta soma aiki a kamfanin Microsoft mallakin Bill.
Su na da yara uku kuma tare suke tafiyar da gidauniyar Bill da Melinda Gates.
Ƙungiyar ta kashe dimbin bilyoyin kuɗaɗe wajen yaƙi da cutuka da karfafa rigakafi ga yara.
Gidauniyar - da mai zuba jari Warren Buffett - ta samar da wani tsarin tallafi, da ke kira ga attajirai su mayar da hankali wajen fida kaso mai yawa na arzikinsu a fanin ayyukan masu kyau.
Bill Gates shi ne mutum na 4 mafi arziki a duniya, a cewar mujallar Forbes, ya mallaki $124bn (£89bn).
Ya samu kuɗaɗensu ne ta kamfanin da ya samar a 1970, Microsoft, kamfanin manhaja mafi girma a duniya.
Sakon mutanen biyu a shafinsu na Tuwita na kan rabuwar ta su na kunshe da wasu bayanai.
"Sama da shekaru 27 na auratayarmu, mu haifa da tarbiyar da yara uku da kafa gidauniyar da ke aiki a ko ina a duniya domin taimakawa mutane samun ingantaccen lafiya, da rayuwa mai inganci," a cewar su.
"Muna da yardar cewa zamu ci gaba da aiki tare domin cimma muradanmu da ayyukan gidauniyarmu, amma muna da yardar cewa ba za mu iya ci gaba da rayuwa tare a matsayin ma'aurata ba a rayuwar.
"Mun nemi saukakawa juna saboda iyalinmu yayinda mu ke shirin soma sabon babbi a rayuwarmu,"
Ya haduwar su ta kasance?
Melinda ta soma aiki a Microsoft a matsayin manaja a 1987, kuma a wannan shekarar mutanen biyu suka zauna domin tattaunawa a liyafar cin abinci a New York.
Daga nan soyayya ta shiga tsakani, amma kamar yada Bill ya shaidawa wani shirin Netflix: "Muna damu da juna sosai kuma sai ya kasance mun shiga wani yanai na zabi biyu: wato, ko mu rabu ko mu yi aure."
Melinda ta ce ta tsinci Bill - cikin wani yanayi na tababa a zuciyarsa - yana nazari da rubuce-rubuce kan alfanu da rashin alfanun yin aure".
Sun yi aure a 1994 a tsibirin Hawaiian da ke Lanai, rahotanni na cewa sun yi hayar dukkanin jirage helikwafta domin hana bakin da ba a gayyata ba isa gare su.
Bill Gates ya bayar mukaminsa na Microsoft a shekarar da ta gabata domin mayar da hankalin kan ayyukansa na agaji.