Batun cewa an murkushe 'yan kungiyar Boko Haram labari ne kawai.
Wata bakwai bayan zamowarsa shugaban kasa a karon faro a shekara 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya fara ikirarin hakan, amma sai dai har yanzu kungiyar na ci gaba da ayyukanta.
Sojojin sun yi kokarin kwato wasu yankuna tare da fatattakar mayakan daga wasu wuraren da suke buya. Amma munin da rikicin ya sake yi a baya-bayan nan a arewa maso gabas, inda a can kungiyar da ke ikirarin kafa daular Musuluncin ta fara ayyukanta a shekarar 2009, ya sa mutane da dama na tambayar abin da ya sa har yanzu hukumomi suka gaza shawo kan matsalar.
A shekarar nan kawai hare-hare kusan 100 aka kai kan fararen hula da sojoji, a cewar wani kiyasi. An kashe daruruwan mutane, sannan an sace makamai da kayayyakin abinci da magunguna.
Kwararru sun ce akwai dalilai shida da suka sa aka kasa murkushe kungiyar duk da ikirarin gwamnati.
1: An kasa magance matsalolin da aka gano
Dogaron da aka yi sosai a kan tsarin soji wajen fuskantar Boko Haram na daga cikin abin da ya sa gwamnati ta kasa shawo kan wannan barazana, kamar yadda wani mai sharhi kan tsaro na kamfanin Beacon Consulting, Kabiru Adamu ya ce.
Ya shaida wa BBC cewa: "Shi ya sa abin takaici fiye da shekara 12 da fara yakin, har yanzu ba a ganin wasu manyan nasarori."
"Kwarai, sojojin na iya fatattakar 'yan ta'addan amma har yanzu suna iya aiwatar da ayyukansu, suna iya daukar sabbin mayaka, suna iya samun kudade, suna kuma iya samun makamai, sai su sake yin karfi."
Kwararru sun ce ba wai mutanen yankin arewa maso gabas na goyon bayan Boko Haram da ISWAP ba ne, amma ko oho din da hukumomi ke nunawa da kuma tashin hankalin da suke shiga ya sa a wasu lokutan mutane kan fada hannun mayakan.
"Maganar gaskiya ita ce idan ana so a magance ta'addanci, ana bukatar fiye da ayyukan soji. Dole sai an magance ainihin matsalar da ta jawo rikicin," a cewar Malam Adamu.
"Sai dai ba mu ga wani abin kirki da aka yi kokarin yi ba a wannan bangaren."
Ya yi nuni da cewa rashin shugabanci nagari ya sanya mutane da dama cikin kunci da damuwa da hana su damar samun ilimi a matsayin "wasu manyan dalilan da suka jawo lamarin."
Akwai manyan tsare-tsaren gwamnati da aka samar don su sa a yi saurin samar da ci gaba a arewa maso gabas, amma ba a cimma wani abin a zo a gani ba.
Sannan akwai matakin yaki da ta'addanci da aka samar na National Counter-Terrorism Strategy, wanda ya hada da ci gaban tattalin arziki da sauya dabi'un mutane da kuma ci gaba da kai dakaru. Amma Malam Kabiru ya ce ga alama ba a amfani da matakin sosai.
Wasu masu sharhin kamar Bulama Bukarti na Cibiyar Kawo Sauyi ta Tony Blair, ya ce bayan sauya dabi'un mayakan Boko Haram da suka mika wuya, ya kamata a ga karuwar ayyukana soji kamar irin yadda aka gani a Iraki da Syria a lokacin da aka murkushe kungiyar IS.
2: Yadda Boko Haram ke iya daukar mayaka
Tsananin talaucin a wasu sassan yankin da kuma salon mugunta da mayakan ke bi sun sa mutane na ci gaba da shiga kungiyar a mataki-mataki, a cewar masu sharhi.
"Mutane a shirye suke su shiga kungiyar kawai don su rayu," a cewar wani masanin tsaro Abdullahi Yalwa, inda yake ba da misalai da matsalar aikin yi da rashin shugabanci nagari.
Mista Bukarti ya ce nuna "yadda ake tilasta wa matasa da karfi"
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum kwanan baya ya shaida wa BBC cewa mayakan suna samun mabiya daga cikin mutanen da rikicin ya tursasa wa barin gidajensu, zuwa cikin kungiyar.
3: Rashin kayan aiki
Ko da an zo batun yakin ma to akwai matsakar makamai, a cewar Mista Adamu, wanda ya ce sojojin ba su da kayayyakin aiki.
Wani bincike da kamfaninsa na Beacon Consulting ya yi, ya gano cewa kusan makamai miliyan 6.5 manya da kanana ne suka bazu a Najeriya, amma 586,000 ne kawai ke hannun jami'an tsaro.
Ba wai ana nufin ko masu tayar da kayar bayan ne suke amfani da sauran ba, amma adadin ya nuna cewa akwai makamai masu yawa da ba sa hannun sojoji.
Malam Adamu ya kuma ce "abin da muke ganin bisa hujjoji shi ne wadannan kungiyoyin 'yan ta'addan suna da manyan makaman da ko sojoji ba su mallaka ba."
4: Cin hanci
Cin hanci na daya daga cikin abubuwan da ke hana samun ci gaba a rundunar soji idan aka zo batun samar da kayan aiki. Ana zargin cewa makudan kudaden da ake kashewa don yaki da Boko Haram a karshe na shige wa aljifan jami'ai ne.
Mista Yalwa ya ce a wasu lokutan ba a yaki da Boko Haram tsakani da Allah kuma wasu mutanen sun mayar da abin kasuwanci da arzurta kansu.
A shekarun baya-bayan nan, an durkusar da rundunar sojin saboda takunkumin makamai da Amurka ta sanya kan keta hakkin dan adam. Shugaba Buhari da tsohon shugaban da ya gada Goodluck Jonathan, dukkan su sun yi korafi kan yadda matakin yake kawo cikas ga kokarin dakile ta'addanci.
Amma Shugaba Donald Trumo ya dage hakan a shekarar 2018 kuma a sakamakon haka Najeriya na sa ran isowar jirgin yaki na Super Tucano. Hakan zai taimaka kan karfin rundunar sojin sama, wadda Mista Adamu ya yi amannar ba a amfani da ita yadda ya dace.
Duk da cewa akwai ikirarin cewa kwalliya ba ta biyan kudin sabulu ta fannin rundunar sojin saman ma.
5: Tsarin soji ba ya aiki
Mr Bukarti ya shaida wa BBC cewa mayakan "sun karanci tare da kwaiwayon yadda sojoji ke kai hare-haren sama" suna kuma amfani da yanayin yankin arewa maso gabas mai sarkakiya wajen kauce wa hare-haren sojoji.
Boko Haram atakaice:
- An kafa ta a shekarar 2002
- Da farko ta fara adawa ne da Ilimin Boko
- Sun kaddamar da fara kai hare-hare a shekarar 2009
- Hankalin duniya ya koma kan kungiyar a shekarar 2014 bayan sace 'yan matan Chibok
- Ta nuna goyon baya ga kungiyar IS a shekarar 2015
- Ta rabu biyu a shekarar 2016.
Akwai kuma wasu bangarorin matakan da su ma ake sukar su.
Cikin fiye da shekara daya da ta gabata rundunar soji tana ta janye dakaru daga kananan sansanoni tare da mayar da su manyan sansanoni da ake kira Super Camps.
A farkon shekarar 2020 ne aka dauki wannan matakin, a lokacin da ake yawan kai wa sojoji hare-hare sannan aka lalata makamansu.
Masu sharhi sun ce hakan ya jawo an bar al'ummomi da yawa kara zube ba tare da tsaro ba.
Malam Adamu ya ce: "Muna da hujja da ke nuna karuwar hare-haren da ake kai wa al'ummomi tsakanin lokacin da aka kirkiri sansanonin Super Camps a yanzu. A bayyane yake cewa kirkirar Super Camps ya bar al'ummomin wasu kauyuka cikin tagayyara," in ji shi.
Hakan kuma ya tagayyara yanayin zamantakewar mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya da suka dogara a kan kamun kifi da noma, kuma hakan na tasiri kan samar da abinci.
Sannan rundunar soji tana da nakasu wajen tattara bayanan sirri da kuma hana kwarmata sirrukanta.
Hakan na nufin a wasu lokutan 'yan ta'addan sun sha gaban sojoji wajen irin hakan," a cewar Mista Yalwa.
Rundunar soji ta yi watsi da ikirarin wannan matsala. Mai magana da yawun rundunar sojin Mohammed Yarima a baya-bayan nan ya ce: "dakarun na cikin azamar yin yaki kuma a shirye suke wajen fatattakar mayakan daga yankin tare da murkushe su baki daya."
6: Tasirin Boko Haram na ƙara yaɗuwa
Wani ƙalubalaen na ƙoƙarin kawar da Boko Haram shi yadda ayyukanta da a arewa maso gabas ke yaɗuwa.
Akwai damuwa kan cewa wasu manyan kungiyoyin tayar da kayar baya a wasu yankunan arewaci da tsakiyar kasar da ke kulla alaka da Boko Haram.
A bara, Boko Haram ta saki wani bidiyo da ke ikirarin cewa ta shiga jihar Neja, wacce ke da nisa daga ainihin yankin da ta saba gudanar da ayyukanta.
Hukumomi sun fitar da sanarwa a watan Maris da ke cewa mayakan Boko Haram sun shiga jihar tare da mamaye dazuzzukan da ke cikinta suna kai hare-hare kan al'ummomin.
A watan Disamba, tsohon hafsan rundunar sojin kasa Laftanal Janar Tukur Buratai ya ce ana iya shafe shekara 20 nan gaba ana yaki da kungiyar Boko Haram, idan har ba a hada kai wajen daukar matakan soji da fararen hula ba.
Mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya ba za su yi fatan yakin ya tsawaita haka ba.