Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Najeriya daga London a ranar Alhamis da yamma.
Mai taimaka wa shugaban kan yada labarai Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC labarin.
Shugaba Buharu ya tafi birnin Londan da ke kasar Birtaniya ne ranar 30 ga watan Maris domin a duba lafiyarsa.
Shugaba Buhari ya sha yin irin wannan tafiya don jinya ko duba lafiyarsa, "don haka ba sabon abu ba ne," kamar yadda Garba Shehu ya fada gabanin tafiyar shugaban.