BBC Hausa of Sunday, 4 April 2021

Source: BBC

Carabao Cup: Yan kallo 8,000 za a bari su shiga wasan

Wannan ne gwajin farko da za a yi na barin 'yan kallo masu yawa su shiga filin kwallo Wannan ne gwajin farko da za a yi na barin 'yan kallo masu yawa su shiga filin kwallo

Za a bar 'yan kallo 8,000 su shiga kallon wasan karshe na kofin Carabao da za a buga tsakanin Tottenham da Manchester City.

Wannan ne gwajin farko da za a yi na barin 'yan kallo masu yawa tun bayan dakatar da shiga filayen wasa a Ingila.

Za a raba tikitin shiga wasan tsakanin magoya bayan kungiyoyin biyu a wasan da za a buga a filin kwallo na Wembley a ranar 25 ga watan Afrilu.

Za kuma a sayarwa da sauaran masu kallo abin da ya yi saura na tikitin.

Ricky Parry, shi ke jagorantar hukumar shirya lig ta Ingila ya ce wannan wata gagarumar nasara ce.

A ranar 18 ga watan Afrilu, za a bar 'yan kallo 4,000 su shiga wasan daf da nakarshe da za a buga tsakanin Leicester City da Southampton.

A ranar 15 ga watan Mayu kuma da za a buga wasan karshe za a bar mutum 21,000 su shiga kallo.

A wasannin ne tsa a fara gwada shaidar karbar rigakafin korona, ga wanda duk sakamakon ya nuna ba shi da cutar to zai shiga filin wasa.