BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

Champions League: Liverpool za ta kara da Leipzig a Budapest

Kocin Liverpool Jurgen Klopp Kocin Liverpool Jurgen Klopp

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA, ta sanar cewar Liverpool za ta karbi bakuncin RB Leipzig karawar zagaye na biyu a Champions League a Budapest maimakon Anfield.

A watan jiya kungiyoyin suka buga wasan farko a Hungary, wanda Liverpool ta yi nasara da ci 2-0, kuma Mohamed Salah da Sadio Mane ne suka ci mata kwallayen.

Sun kuma fafata ne a Budapest, sakamakon Jamus da ta kafa dokar hana shiga kasarta ga wadanda cutar korona ta yi kamari a wajen su har da Burtaniya.

Saboda haka filin da ake kira Puskas Arena shi ne zai kara karbar bakuncin fafatawa ta biyu ranar 10 ga watan Maris a matsayin gidan Liverpool.

Wannan sauyin wurin buga wasan bai shafi ranar da za su kara ko lokacin da za su fafata ba da aka tsara tun farko.

Sai dai kuma UEFA ta sanar da cewar Manchester City za ta iya karbar bakuncin Borussia Monchengladbach a Etihad kamar yadda aka tsara a baya.

City da Gladbach sun buga wasan farko a Budapest fafatawar zagaye na biyu a Champions League ranar 24 ga watan Fabrairu.

Kuma City ce ta yi nasara da ci 2-0, inda Bernardo Silva da kuma Gabriel Jesus suka ci mata kwallayen.

City za ta karbi bakuncin Gladbach ranar 9 ga watan Maris, bayan da dokar hana yada cutar korona take da sauki a yankin Arewacin Rhine- Westphalia inda Glabdach take fiye da ta Saxona wajen da Leipzig take.