BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Chelsea ba za ta hukunta Rudiger da Kepa bayan da suka yi rikici

Antonio Rudiger tare da Kepa Arrizabalaga Antonio Rudiger tare da Kepa Arrizabalaga

Thomas Tuchel ya yaba da halin girma da mai tsaron baya, Antonio Rudiger da mai tsaron raga, Kepa Arrizabalaga suka nuna, bayan rikici a tsakaninsu ranar Lahadi.

Rudiger dan wasan Jamus ya yi karo da mai tsaron ragar da ta kai aka umarce shi ya koma dakin sauya kaya, bayan da Arizabalaga ya fusata suka cukumi juna sai da aka shiga tsakani.

Kocin Chelsea ya ce lamarin mai girma ne, amma kungiyar ba za ta hukunta su ba, domin a lokacin atisaye kuskure kan auku a kowanne lokaci.

Ranar Asabar aka kawo karshen wasa 14 da Chelsea ta yi ba a doke ta ba karkashin Tuchel, bayan da West Bromwich ta yi nasara da ci 5-2.

Sai dai kocin dan kasar Jamus ya bukaci magoya bayan Chelsea su kwantar da hankali dangane da shirin fuskantar FC Porto a Champions League ranar Laraba da za su yi.

Ranar Laraba ne Chelsea za ta ziyarci Portugal a wasan farko karawar daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai.

Haka kuma Tuchel ya tabbatar cewar Christian Pulisic yana cikin 'yan wasan da Chelsea za ta je da su Portugal da kuma N'Golo Kante da zai yi zaman benci ranar Larabar.

Chelsea tana ta biyar a teburin Premier League da maki 51 da tazarar maki daya tsakaninta da ta hudu West Ham United.