BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Chelsea ta kare Premier League ta bana a mataki na hudu

Kocin Chelsea Thomas Tuchel Kocin Chelsea Thomas Tuchel

Chelsea ta samu gurbin shiga gasar Champions League ta badi duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa da ci 2-1 a gasar Premier karawar mako na 38.

Chelsea ta shiga karawar mako na 38 ranar Lahadi a gasar ta Premier a mataki na uku, inda Liverpool ta hudu, sannan Leicester City ta biyar.

Bertrand Traore ne ya fara ci wa Chelsea kwallo daf da za su je hutu, sannan Anwar El Ghazi ya ci na biyu a bugun fenariti bayan hutu.

Kafin a ci Chelsea kwallo na biyu, mai tsaron ragarta Edouard Mendy ya yi rauni, inda ake cewa watakila ba zai iya kama gola a wasan karshe na Champions League da Manchester City ba.

Nan da nan ta saka Kepa Arrizabalaga ya maye gurbinsa, wanda aka ci kwallo na biyu a bugun fenariti.

Daga baya ne Chelsea ta zare kwallo daya ta hannun Ben Chilwell, saura minti 20 su tashi daga wasan.

Chelsea ta karkare karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Cesar Azpilicueta jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Jack Grealish na Aston Villa.

Kungiyar Stamford Bridge ta kammala gasar Premier ta bana a mataki na hudu da maki 67, ta kuma samu damar ce, bayan da Tottenham ta doke Leicester da ci 4-2.

Liverpool wadda ta doke Crystal Palace 2-0 a Anfield, ita ce ta uku da maki 69, ita kuwa Leicester mai maki 66 tana ta biyar za ta buga Europa League kenan.

Daman tuni Leicester ta samu gurbin Europa League tun bayan da ta yi nasara a kan Chelsea da ci 1-0 a wasan karshe a FA Cup a Wembley.

Chelsea za ta buga wasan karshe da Manchester City a Champions League ranar Asabar 29 ga watan Mayu a Portugal.