BBC Hausa of Sunday, 30 May 2021

Source: BBC

Clubhouse: Mene ne shi kuma ta yaya ake shiga?

Clubhouse wata manhaja ne na daban domin ana anfani da murya ce kawai Clubhouse wata manhaja ne na daban domin ana anfani da murya ce kawai

Ƙasa da shekara daya, Clubhouse ya kai ya kawo a matsyainsa na abin da ake yayi:

  • ƙaurin suna


  • shararrun mutane


  • janyo ce-ce-ku-ce


  • haramtawa


  • samun karɓuwa duk da cewa ba ya samun kuɗin shiga


  • Ga abubuwan da ya kamata ku sani.

    Me ya sa zan damu da shafin?

    Ana ta magana a kan shafin a faɗin duniya, daga Amurka (indaaka ƙirƙiri manhajar) zuwa China da Brazil da Turkiyya.

    Duk inda ku ke a faɗin duniya, babu mamaki kwanan nan za ku fara ji ana maganarsa.

    Wasu daga cikin shahararrun mutane a duniya na amfani da shafin:

    Kuma babu shakka wannan tururuwar da ake yi wa shafin dole kuɗi ya biyo baya, inda masana ke ganin darajar Clubhouse ta haura dala biliyan 1, a cewar jaridar Financial Times.

    Ya Clubhouse ke aiki?

    Abin da ya sa manhajar ta fita daban shi ne rashin rubutu da hotuna da bidiyo.

    Murya ce kawai.

    Haka kuma, komai kai tsaye ya ke faruwa a shafin.

    Kana iya buɗe 'ɗaki' da kanka ko kuma ka shiga wani inda mutane ke magana.

    Akwai iya adadin mutanen da za su iya magana.

    Duk sauran mutanen sai dai su saurara.

    Amma kana iya 'ɗaga hannunka' ka buƙaci a ba ka damar yin magana.

    A cikin manhajar, ba a naɗar hirar da ake yi ko kuma a ajiye ta don saurare daga baya.

    Don haka dole ka saurari komai alokacin da ya ke gudana.

    Me ya sa shafin ya fita daban?

    Shafin mai amfani murya zalla na bayar da kusanci ga mai amfani da shi kamar na sauraren shirin rediyo.

    Kuma duk da cewa mutane na mafni da manhajar ne kawai don su yi magana da abokansu, kana iya sauraren shaharrarun mutane kamar Elon Musk mai kamfanin Tesla da SpaceX suna hira ta yau da kullum kamar kana cikin ɗaki ɗaya tare da su.

    Wani tagomashi da ba ariga an hango ba dangane da shafin, shi ne ya yi ƙoƙarin kauce wa takunkumin da gwamnatoci ke sa wa manyan shafukan sada zumunta.

    Amma an riga an haramta amfani da shi a China.

    Shafin yaɗa labarai Quartz ya ruwaito cewa ƴan China masu amfani da Clubhouse sun daɗe "suna amfani da shafin wajen magana kan batutuwan da za a zahiri za a hana su...kamar dimokuraɗiyya", wannan ya sa aketa tururuwar yin rajista a shafin.

    Haka kuma, wasu shafukan sun fara ɗaukar salon Clubhouse na amfani da murya kawai.

    Zan iya sauke shi yanzu?

    Ba a amfani da shi a kan wayoyin Huawei da Samsung da LG da sauran wayoyin Android.

    Kuma ko masu amfani da wayar iPhone ba za su iya kawai shiga hirar wasu bayan sauke manhajar.

    Kana iya shiga Clubhouse ne kawai idan aka gayyace ka.

    Da farko, masu amfani da manhajar na da damar gayyatar mutum biyu ne kawai.

    Amma wannan ba ya nufin ba zai nufo ku nan kusa ba.

    Kamfanin na aiki wajen ganin an buɗe manhajar ga kowa da kowa.

    Mene ne illolinsa?

    Kamar ko wane shafin sada zumunta a tarihi, Clubhouse na fuskantar tantama dangane da ɓoye sirri.

    Kamfanin ya ce yana bitar wannan bayan wani bincike daga jami'ar Stanford ya nuna cewa ana aika bayanan masu amfani da shafin zuwa komfutoci a China.

    Haka kuma, yana fama da matsalar da wani ya bankaɗo cewar akwai hanyar da ake iya bi a tattaro hirarrakin da aka yi a ɗakuna da yawa a shafin sannan a wallafa su a wasu shafukan na daban

    "Clubhouse ba zai iya yin wani alkawari dangane da tsare sirrin hirar da ake yi a shafin a ko ina a faɗin duniya ba," a cewar wani jami'in ɓangaren Kula da Intanet ba Stanford Alex Stamos.

    Ga mafi yawan masu amfani da shafin, wannan ba zai zama matsala ba tunda shafin dama na hira ne da samun mutanen da za su saurara kai tsaye.

    Amma kuma babu abin da ya hana wani daga cikin masu sauraren hirar naɗarta a lokacin da ake gudanar da ita.

    Zai zama shafin sada zumunta mafi shahara?

    Clubhouse na da masu amfani da shi miliyan biyu kawai.

    Yana ci gaba da samun masu sauke shi.

    Amma sana'ar shafukan sada zumunta ba ta da tabbas.

    At first glance, Clubhouse appears simply to be a good idea with no proprietary technical tricks behind it.

    And that means it can easily be copied by its competitors.

    Twitter is already working on its own version of rooms, called "spaces".

    So Clubhouse does not have long before more established players may start muscling in.

    Da farko, ana iya ganin Clubhouse a matsayin abu mai kyau ba mai wasu matsaloli ba.

    Kuma wan na nufin masu gogayya na iya kwafarsa.

    Twitter