BBC Hausa of Tuesday, 4 May 2021

Source: BBC

Coronavirus: Me ya sa wasu masallatai ke hana mata ibada a watan Ramadan?

Wasu masallatai a Birtaniya na hana mata shiga domin yin sallah Wasu masallatai a Birtaniya na hana mata shiga domin yin sallah

Miliyoyin Musulmai na yin ibadar azumin Ramadan a faɗin duniya a yanzu haka. Sai dai wasu masallatai a Birtaniya na hana mata shiga domin yin sallah, yayin da a gefe guda kuma wasu ke cewa lokaci ya yi da za a samu sauyi.

Da kyar Almas ke samun lokacin yin ibada. Bazawara ce mai 'ya'ya uku kuma tana karatun digiri a jami'a. Dalilin da ya sa kenan take kallon Ramadan a matsayin wata dama ta musamman.

"Na yi ta hanƙoron fara sallar Tarawihi musamman a ƙarshen mako, lokacin da muke da isasshen lokaci," a cewarta. "Sai dai da na tuntuɓi masallacin unguwarmu sai suka ce 'ban da tsofaffi, ban da yara, ban da mata'."

Ba Almas kaɗai ba, sauran masallatai da yawa a faɗin Birtaniya sun yanke shawarar hana mata shiga a wannan watan. Akasari sukan ce saboda annobar korona.

Mata irinsu Almas ba wai sallar Tarawihi kaɗai suke gaza yi ba, wadda nafila ce da ake yi a watan Ramadan, da yawa ba sa iya yin ibadar ma gaba ɗaya a masallatai, ciki har da Juma'a.

'Marasa gata'

Yayin da iyalai da dama ke yin sallarsu a gida, da alama ibada a masallatai na ta'allaƙa ne da jinsin mutum, inda mutane da yawa ke ganin cewa hakan yana ba da damar natsuwa wajen gudanar da ibadar ga maza.

Wani lokaci mata kan yi sallah a bayan maza a wuri ɗaya. Sai dai akasari akan samar da ɗaki biyu ne na maza daban na mata daban, yayin da maza ke yin sallah a ainahin masallacin su kuma mata a keɓaɓɓen wuri kuma ƙarami.

Amma ba duka masallatai ne ke ware wurin mata ba. Fiye da ɗaya cikin huɗu na masallatai a Birtaniya ba su da ɓangaren mata. A wuraren da babu ɓangaren mata, akasari girman wurin yana bambanta.

Anita Nayyar, wadda ke fafutikar Open My Mosque don nema wa mata 'yancin addini, ta ce da yawa ana bai wa mata "kujerar baya" ne. ta ce ɓangarensu ya yi ƙanƙanta, inda ake ba su wurare kamar gidan ƙasa ko kullellun ɗakuna ko kuma fili fetal.

Ita ma annobar korona ta ta'azzara lamarin.

"A lokacin dokar kulle, mun samu rahotanni cewa masallatan da mata ke zuwa sun hana su shiga, ko dai don su bi dokokin bayar da tazara ga maza ko kuma dai ba za su iya tabbatar da dokar ba a ɓangaren matan," in ji ta.

BBC ta tuntuɓi manyan masallatai guda 29 a Birtaniya domin jin tsare-tsarensu na watan Ramadan.

Biyar dagaa ciki ba su da ɓangaren mata, yayin da shida suka ce ba za su iya barin mata ba saboda kariya daga annobar korona. Guda 12 sun bar mata, amma bakwai daga ciki ba su ba mu amsa ba.

Daga cikin masallatan akwai Greenwich Islamic Centre da Baitul Futuh na Landan da Jamia Al-Akbaria da ke Luton Masallacin Lanarkshire da ke Scotland.

Masallacin su Almas mai suna Milton Keynes Islamic Centre bai amsa buƙatar BBC ba da farko, amma daga baya ya ce ya hana mata da yara da tsofaffi shiga yayin wani "matakin gwaji".

"Abin haushi shi ne akwai ɓangaren mata da kuma manyan ɗakuna uku a ƙasa," Almas ta bayyana. "Akwai matan da na sani a masallacin waɗanda zawararwa ne da ba sa tare da yaransu da kuma masu fama da lalurar ƙwaƙwalwa.

"Yadda abin ke damuna, ina mamakin yadda zai dami sauran waɗannan matan su ma."

"Abu neda za a iya yi"

Julie Siddiqi, wata mata mai fafutikar sama wa mata masallatai a Birtaniya, ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram tana kokawa kan yadda masallacin unguwarsu Jamia Masjid and Islamic Centre suka ƙi barin mata shiga a Ramadan ɗin nan.

Ɗaruruwan mata a Birtaniya sun tura mata saƙon cewa su ma suna fuskantar irin wannan halin.

"Na fahimci cewa akwai maganar kiwon lafiya," in ji ta. "Amma masallacinmu na da girma sosai. Abu ne mai yiwuwa a masallacin. Magana ta gaskiya wannan abin ya fi ƙarfin korona. Da gangan ne kawai, aƙida ce cewa maza ne za su yanke hukuncin ko mata za su iya zuwa masallaci ko a'a."

Masallacin nata sun faɗa wa BBC cewa sun ɗaukji matakin ne bayan sun tuntuɓi wasu mata 'yan sa-kai "waɗnda ke da burin haɓaka harkokin mata". Ya ce ba zai so ya saka masu fafutikar cikin haɗari ba.

Masallacin Baitul Futuh da ke Landan ya ce ba "wajibi ba ne a Musulunci mata su yi sallar jam'i a masallaci, wajibin na maza ne".

Musulunci ya sharɗanta cewa sallar jam'i dole ce maza, amma ba dole ba ce kan mata waɗanda za su iya yin ta a gida.

"Da zarar an cire dokokin kulle mata za su ci gaba da zuwa masallaci don gudanar da ibadu," a cewar masallacin cikin wata sanarwa.

Sheikh Ibrahim Mogra, wani limami a Leicester, ya ce "ya kamata a bai wa maza da mata damar shiga masallaci", yana mai cewa: "Wasu malaman sun ce zai fi kyau mata su yi sallah a gida fiye da masallaci, saboda haka akwai saɓani."

Wasu masallatan sun sauya shawara. Da farko Masallacin Hounslow Jamia Masjid and Islamic Centre ya tsara maza ne kawai za su yi sallah, amma ya sauya bayan an fara tattauna matsalar rashin zuwan mata masallataia a intanet a farkon Ramadan.

Zara Mohammed, shugabar ƙungiyar Musulmai ta Birtaniya, ta ce kiran da suke yi shi ne a bai maza da mata damar amfani da masallaci - "a watan Ramadan ko kuma wajensa".

"Dole ne a saka mata cikin shirin tafiyar da masallatai kuma muna ƙarfafa gwiwar ci gaba da tattaunawa mai amfani domin samar wa mata ƙarin damarmaki."