BBC Hausa of Friday, 12 March 2021

Source: BBC

Covid-19: Abu 8 da muka koya shekara ɗaya bayan ɓullar annobar cutar

Anyi shekara ɗaya bayan ɓullar annobar cutar COVID-19 Anyi shekara ɗaya bayan ɓullar annobar cutar COVID-19

Lokacin da aka fara gano bullar kwaya cutar korona ko kuma Covid-19 (Sars-CoV-2) shekara daya da ta gabata, kwayar cutar ta rikirkita lissafi da tunanin masana kimiyya, da likitoci da marasa lafiya.

Bayan shekara guda, annobar ta lakume rayukan mutane fiye da miliyan daya da rabi tare da yaduwa kan mutane miliyan daya da dubu dari goma sha bakwai a fadin duniya (daga 10 ga watan Maris), an kuma yi tunanin cewa za ta dan yi sauki.

Amma kuma a daidai wannan lokacin, likitoci, da masana kimiyya sun samu manyan shaidu game da sabn mau'in cutar korona - kuma yanzu mun san yadda take yaduwa, da kuma yadda za a iya magance ta cikin sauki.

Ga wasu manyan abubuwan takwas da muka koya game da cutar ta korona:

1. Takunkumin fuska na da muhimmanci wajen rage yaduwar cutar korona

Saka takunkumin fuska kadai ba zai iya yin kariya daga yaduwar cutar korona ba, amma kuma yana taimakawa matuka wajen rage yaduwar ta, kamar yadda bincike da dama suka nuna.

A baya-bayan nan, Cibiyoyin Kula da Dakilewa da Rigakafin kamuwa cututtuka (CDC) a Amurka, sun ce saka takunkumin fuska mai inganci sosai ( na kyalle a kan na asibiti) ka iya rage yaduwar kwayar cutar da kashi 90 bisa dari.

Kamar yadda kwararru suka bayyana, takunkumin fuska na da muhimman abubuwa akalla biyu: kariya ga wadanda suka saka, da kuma kariya ga wadanda suka zo kusa da wanda ya kamu kuma yana sanye da takunkumin.

Tun a cikin watan Yuni, Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta goyi bayan amfani da takunkumin fuska na kyalle ga duka mutane da ke bukatar fita daga gida.

A cikin watan Disamba, Majalisar Dinkin Duniya ta sabunta amincewarta kana ta yi kira da a tsaurarra fadakarwa game da saka takunkumin fuska, musamman a cibiyoyin kiwon lafiya.

Ita ma cibiyar dakiliewa da rigakafin kamuwa da cututtuka (CDC) ta yi irin wannan furucin a baya cikin watan Aprilu.

A baya-bayan nan, wasu kasashen Turai sun yi gargadin- ko kuma hana - amfani da takunkumin rufe fuskar da aka dinka da kyallayen da aka yi amfani da su a cikin gida, inda ta bukaci amfani da nau'in N95 and PFF2, da ke bayar da ingantacciyar kariya.

"Takunkumin rufe fuskar da aka yi da kyallaye har yanzu suna da amfani, ama su kan kawai kare wasu mutane daga kai ta hanyar rage fitar wasu kananan abubuwa da ka iya fita daga wadanda ska saka,'' Vitor Mori, wani masanin kwayoyin halittu kuma dan kungiyar sa ido kan cutar ta korona ya shaida wa

2. Ba tofaffi kadai cutar korona ke kamawa ba

Barazanar kamuwa da cutar korona mai tsananoi na ta fi yawa ga yawan shekaru, da ke saka tsofaffi ko wadanda suka manyanta cikin barazana.

Dalilin faruwar hakan mai sauki ne kuma bai shafi batun kwayar cutar korona ba: a yayinda muke kara shekaru, garkuwar jikinmu na kara yin rauni, tare da barin jikinmu ba tare da isasshiyar garkuwar da za ta iya fada da kwayoyin cuta ba.

Don haka, ba yana nufin masu kananan shekaru ko matasa suna da garkuwar da za ta hana su kamuwa da cutar ta korona ba, ko wadanda ba su da wata zaunanniyar cuta kamar ciwon suga, da hawan jini, da taiba.

Kamar kowa, matasa za su iya kamuwa da tsananin cutar korona, su bukaci kwanciya a asibiti, ko kuma ma su rasa rayukansu daga cutar.

Kuma duk da cewa barazanar mutuwa daga cutar korona a tsakanin masu kasa da shekaru 50(kuma musamman ma kasa dashekara 30) ana ganin ba ta da yawa.

BBC ta samu bayanai daga ma'aikatan jinya a kasa Spain da suka ce cutar numfashi ko kuma pneumonia da ta samo asali daga cutar korona na kara zama matsanaciya a tsakanin marasa lafiya masu kananan shekaru.

"Kwayar cutar ka iya saka masu kananan shekaru kwanciya a asibiti har na tsawon makonni, ko kuma ma hallaka su,'' Darakta Janar Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa BBC a cikin watan Maris na shekarar 2020.

Ghebreyesus ya kuma yi gargadin cewa duk da matasa ko masu kananan shekaru ka iya kasancewa ba su kau da cutar mai tsanani ba, halayyarsu za ta iya nufin''banbanci tsakanin rayuwa da mutuwa ga wani mutum.''

3. Korona ba 'mura mai sauki ba ce'

Alamun cutar korona ka iya kasancewa iri daya da na mura da muka sani:

    zafin jiki mai tsanani tari kasala
Wasu mutane kan fuskanci ciwon gabobi, da ciwon kai, da yiwuwar yin amai da gudawa.

Kana kamar mura, cutar korona tana iya yaduwa ba tare da nuna alamu ba, ko kuma marasa lafiya ka iya kasancewa ba masu nuna wata alama ba.

Amma kuma, abubuwan da suka biyo bayan cutar korona sun kasance masu tsanani ga mutane da dama.

'Yan siyasa kamar shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ko tsohon shugaban Amurka Donald Trump sun so su boye tsananin da cutar korona take da shi wajen cewa kamar '' mura mai sauki ce'' - amma alkaluman bincike sun nuna cewa duka kasashen biyu sun fadi labarin da suka sha banban da juna.

A Amurka, korona ta kasance kan gaba wajen haddasa asarar rayukan jama'a a cikin watannin baya-bayan nan (mutane sama da 525,000 ne suka mutu a yanzu haka), yayin da a kasar Brazil alkaluma suka nuna cewa mutane 266,000 ne suka mutu ( fiye da yadda cututtukan shanyewar barin jiki, da cutar numfashi ta pneumonia ke haddasawa).

4. Cutar korona ta samo asali ne daga dabbobi (ba daga dakin binciken kimiyya aka kirkiro ta ba)

Tawagar Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO wacce ta binciki asalin kwayoyin cutar Sars da Covid 2 a birnin Wuhan (kasar China) ta ce duka shaidun da aka tattara sun nuna ''dabba'' ce asalin sabuwar nau'in cutar korona.

"Duka bayanan binciken da muka tattara sun kai mu ga gano cewa asalin cutar korona daga dabbobi ne," jagoran tawagar ta WHO Peter Ben Embarek ya shaida wa manema labarai.

Kamar yadda Embarek ya bayyana, shaidu sun nuna cewa sabuwar nau'in cutar korona ta fara samo asali ne daga jemagu: '' Amma wadannan dabbibi ba lallai ne a ce an same su a birnin Wuhan bane.

Da wuya aka iya gano dabbar da ke da alhakin yada kwayar cutar,'' ya bayyana.

Embarek ya ce har yanzu ana cigaba da bincike game da asalin cutar ta korona, amma kuma ya kara da cewa yiwuwar cewar kwayar cutar ta korona ta bullo ne daga dakin binciken kimiyya '' ba lallai ya zama gaskiya ba''.

5. Magugunan Chloroquine da hydroxychloroquine ba sa aiki wajen warkar da cutar korona

A farko-farkon barkewar annobar, an rika tunanin cewa chloroquine - maganin da a al'adance ake amfani da shi wajen warkar da cutar zazzabin cizon sauro - da kuma hydroxychloroquine, za su iya aiki wajen warkar da cutar korona.

Duka tawagar masu bincike na kasashen Chinese da Faransa sun bayyana cewa magungunan ka iya yin aiki, amma kuma tun a lokacin bincike da dama da aka gudanar sun bayana cewa wadannan magunguna ba su da wani amfani ko kuma ma za su iya haifar da damuwa.

A cikin watan Yulin shekarar da ta gabata, kungiyar lafiya ta dniya n July of last year WHO ta dakatar da gwaje-gwaje da maganin hydroxychloroquine bayan da ta gano cewa ba a samu raguwar yawan mace-macen marasa laiya da ska kamu da cutar ta korona ba.

A yanzu haka, babu wata shaida da ta tabbatar da tasirin amfani da wadannan magunguna a kan cutar korona.

6. Za ka iya kamuwa da cutar korona daga zuzzuba abincin kanti a cikin mazubansu

Akon barkewar annobar, dubban mutane sun bayar da rahoto a shafukan sada zumunta game da damuwa kan yadda za a rika kula da tsafta wajen zuzzuba abincin kanti a koda yaushe.

Amma kuma kamar yadda WHO ta bayyana, babu wasu bayanai da aka tabbatar cewa ana yada cutar korona ta hanyar abinci ko ta hanyar yadda ake zuba abincin.''.

Har ila yau, WHO din da fitar da jerin matakai kauce wa yada kwayoyin cuta, kamar amfani da sinadarin goge hannu kafin a shiga shagunan sayar da kaya, da kuma ''wanke hannaye bayan ka dawo gida, bayan taba gwangwanaye ko mazuban abinci, kana kafin cin abinci.''

Hukumar Lura da Igancin Abinci da Magunguna ta Amurk (FDA) ta fitar da wani rahoto da ke muhimmantar da wannan batu, kana ta ce babu tabbacciyar shaida da ta nuna cewa ana yada kwayar cutar korona ta hanyar abinci ko kuma abubuwan da aka zuba abincin kanti.

Don haka kai sakon kayan abinci har gida kada ya zama abin damuwa, amma yana da muhimmanci a rika wanke hannu bayan karbar sakonnin abincin.

Kwararru kuma sun bayar da shawarar amfani da jakunkunan leda sau daya kawai.

7. Za ka iya kamuwa da cutar korona fiye da sau daya

Binciken da hukumar kula da lafiyar al'umma da Birtaniya ta gudanar, ya gano cewa akasarin mutanen da suka kamu da cutar korona kashi 80 bisa dari na da garkuwa ta akalla watanni biyar.

Amma batun sake kamuwa da cutar, duk da ba kasafai yake faruwa ba, a kan samu a kasashe da dama - kuma babbar damuwa ga kwararru a fannin kiwon lafiya ita ce sake kamuwa da sabuwar nau'in cutar.

Muddin adadin mutane da yawa da suka warke daga cutar ta korona suka sake kamuwa, zai iya kasancewa saboda sabuwar nau'in cutar ne.

Akwai dubban nau'uka da dama na kwayar cutar ta korona da ke zagayawa, amma abubuwan da suka fi zama da damuwa su ne:

Ba wani abin ba-zata bane cewa sabbin nau'ukan sun bayyana - duka kwayoyin cuta kan sauya kamanni kana suka sake yin irin kamanninsu su kuma yadu cikin sauri.

Akasarin irin wadannan banbance-banbance ba su da wanu muhimmanci.

Kadan ne su kan zama masu hadari ga rayuwar kwayoyin cutar. Amma wasu kan sa ta zama mai yaduwa da kuma barazana.

A duka abubuwa ukun, nau'in sabuwa, mafi saurin yaduwa na taka muhimmiyar rawa wajen haifar da yawan karuwar masu kamuwa da kuma jinya a asibitoci.

8. Ya kamata alluran rigakafin sun cigaba da aiki a kan sabouwar nau'in kwayar cutar - a yanzu

Ruwan alluran rigakafin an hada su ne saboda nau'in farko na cutar korona, amma maana kimiyya sun yi amanna cewa za su iya aiki, duk da cewa me yiwuwa ba yadda ya kamata ba.

Binciken baya-bayan nan ya nuna cewa nau'in kwayar cutar ta kasar Brazil ka iya bijirewa zaunannun kwayoyin cutar da ke fada da su a jikin mutanen da ya kamata a ce suna da gakuwar jikin saboda sun taba kamuwa da cutar suka warke daga nau'in cutar ta farko.

Sakamkon farko na dakin binciken kimiyya ya nuna cewa magugunan rigakafin kamfanin harhadamagunguna na za su iya yin kariya daga sabuwar nau'in cutar ta korona, duk da cewa ba yadda ya kamata ba.

Sabbin uwan alluran rigakafin cutar korona biyu da za a iya amincewa da su nan ba da dadewa ba - daya daga kamfanin harhada magunguna na Novavax kana daya daga kamfanin Janssen - da alamu su ma za su iya bayar da kariya.

Bayanan da aka tattara daga tawagar hada ruwan allurar rigakafi na Oxford-AstraZeneca sun nuna cewa tana bayar da kariya ga sabuwar nau'in cutar.

Amma kariya kadan ta ke bayar wa nau'in kawayar cuyar ta kasar Afirka ta Kudu - duk da cewa ya kamata da bayar da kariya daga cuta mai tsanani.

Sabon sakamako daga kamfanin harhada magunguna na Moderna ya nuna cewa ruwan allurar na da tasiri kan nau'in kwayar cutar ta kasar Afirka ta Kudu, duk da cewa yanayin garkuwar jikin ba zai kasance yana da karfi ko kuma mai dorewa ba.

Nan gaba za a iya sake samun bullar sabbin nau'ukan kwayar cutar, amma kuma ko a cikin yanayi mai tsanani za a iya sake sabunta ruwan allurar rigakafin da zai dace - a cikin makonni ko watanni, idan bukatar haka a taso, in ji masana.

Me yiwuwa za mu wayi gari muna magance cutar korona kamar yadda muke magance cutar mura, idan aka rika sake samar da sabbin ruwan alluran a ko wace shekara don duna yanayin sauye-sauyen da kayoyin cutar murar kan yi.