BBC Hausa of Tuesday, 6 April 2021

Source: BBC

Cuba: Masu suka na gamuwa da fushin gwamnati

Cuba: Masu suka na gamuwa da fushin gwamnati Cuba: Masu suka na gamuwa da fushin gwamnati

Jami'an tsaro a Cuba sun kama wani fitaccen mai sukar gwamnati, Luis Manuel Otero Alcántara, a wani mataki na kame masu sukar lamirin gwamnati a fadin kasar.

An tsare 'yan hamayya da dama tare da 'yan uwa ko iyalansu a 'yan kwanakin da suka gabata, yayin da gungun wasu 'yan hamayya a gabashin tsibiri ya shiga yajin cin abinci, domin tabbatar da ganin an yi wasu tarin sauye-sauyen siyasa a kasar mai bin tsarin gurguzu.

Tarin 'yan kungiyar San Isidro da suka yi fice wajen sukar gwamnatin Cuban sun bukaci hukumomi a kasar da su yi musu bayani kan inda daya daga cikin mambobinsu, fasihi Luis Manuel Otero Alcántara, yake.

Magoya bayansa sun ce sun yi amanna yana tsare a hanun jami'an tare da wasu masu sukar gwamnatin biyu, kuma suna bukatar da a sake su ba tare da bata wani lokaci ba.

Hakan na kasancewa ne yayin da dangantaka ke kara tsami tsakanin masu sukar da kuma hukumomin kasar.

A Santiago, da ke yankin gabashin tsibirin, 'yan wata fitacciyar kungiyar masu hamayya da gwamnatin, UMPACU, sun shiga yajin aikin cin abinci fiye da mako daya, inda wasu rahotanni ke cewa wasu daga cikin shugabannin kungiyar na cikin tsananin galabaita saboda rashin cin abincin.

Gwamnatin kasar ta Cuba na zargin dukkanin kungiyoyin biyu da zama karnukan farautar gwamnatin Amurka.

Can a Havana babban birnin kasar an 'yan kungiyar Isidro Movement sun yi dauki-ba-dadi da 'yan sanda a kofar hedikwatar kungiyar,

yayin da jami'an suka je domin kama wani mai sukar wanda mawaki ne na zambo Maykel Osorbo. Mutane da dama da ke kusa sun dauki hotunan bidiyo na dambarwar a waya, inda ake iya gani tirjiyar yayin da magoya bayan kungiyar ke wakoki suka da rera take na cin zarafin shugabancin kasar ta Cuba.