BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Cyrptocrash: Dalilan da suka sa darajar Bitcoin ta faɗi

Darajar Bitcoin ta faɗi Darajar Bitcoin ta faɗi

Beijing ta haramta wa bankuna da kamfanoni biyan kudade daga gudanar da ayyukan da suka shafi mu'amala da kudin na Bitcoin.

Ta kuma gargadi masu zuba jari a kan batun huddar cinikayyar ta kudin na intanet a ranar Talata.

Ya biyo bayan faduwar darajar Bitcoin din da fiye da kashi goma bisa dari (10%) a makon jiya bayan da kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki Tesla ya ce ba zai cigaba da amincewa da karbar kudin na intanet ba.

A ranar Laraba ne, Bitcoin din ya sake farfadowa, duk da cewa har yanzu yana kasa - kashi goma da kadan bisa dari (10.4%) a dala dubu talatin da takwas da dari da talatin da daya ($38,131).

Ta wani gefen kuma, sauran kudaden intanet kamar su Ether, da Dogecoin sun yi asarar kashi ashirin da biyu bisa dari (22%) da kashi ashirin da hudu bisa dari (24%) daban-daban.

A karon farko cikin watanni uku a ranar Laraba, farashin Bitcoin ya fadi kasa da dala dubu talatin da hudu ($34,000) kwatankwacin fan ashirin da hudu da talatin (£24,030), bayan da kasar China da kafa sabuwar dokar haramci kan amfani da kudin na intanet.

A karo daya, hannayen jarin kamfanin Tesla sun fadi da fiye da kasha uku bisa dari (3%) a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Wall Street, da mai yiwuwa saboda yadda kamfanin kera motoci masu amfani da lantarkin ke mu'amala da kudin na Bitcoin ne.

Kamfanin wanda mallakar Elon Musk ne, har yanzu yana da kadarar kusan dala biliyan daya da miliyan dari biyar na kudin na intanet.

Haramcin Beijing game da Bitcoin

Kasuwancin kudin na intanet ya kasance haramtacce a kasar China tun a shekarar 2019 don kauce wa halarta kudin haram. Amma kuma har yanzu mutane na cigaba da da kudade irin su Bitcoin ta shafin yanar gizon, wanda ya zama babban abin damuwa ga Beijing.

A ranar Talata ne, kungiyoyi uku da gwamnatin kasar ke mara wa baya da suka hada da Kungiyar Hada-hadar Kudaden Intanet ta kasar China, da Kungiyar Harkokin Bankunan kasar China, da kuma Kungiyar Biya da Aikewa da Kudade ta kasar China suka fitar da wata sanarwar gargadi a shafukan sada zumunta.

Sun bayyana cewa masu mu'amala da su da wata kariya idan suka tafka asara daga hada-hadar zuba jari ta hanyar amfani da kudaden intanet din.

Sun kuma kara da cewa hauhawar farashin irin wadannan kudade da aka samu a baya-bayan nan ''sun yi mummunan saba wa kariyar kadarorin jama'a'' kuma suna haifar da kwan-gaba kwan-baya ga '' tsarin kudade da tattalin arziki da aka saba da shi''.

Tesla ya yi amai ya lashe

A cikin watan Maris ne jagoran kamfanin Tesla mai kera motoci masu amfani da lantarki Elon Musk ya yi sanarwar ba-zata cewa zai amince wa masu sayen motocin kamfaninsa su saya da kudin na Bitcoin.

Amma kuma a makon jiya, ya yi amai ya lashi inda ya janye batun sayen motocin da kudin na Bitcoin saboda damuwa game da batun muhalli.

Fargabarsa ta karkata ne kan hakar kudin na Bitcoin - ta hanyar amfani da wutar lantarki mai yawa da ake yi wajen fitar da kudin na intanet da na'urorin komfuta masu jan karfin wutar lantarkin .

A ko da yaushe ana dogara ne da wutar lantarki da kuma makamashin da akan samu daga tsirrai ko wasu halittu, musamman na ma'adanin kwal.

"Mun damu matuka game da yawan amfani da makamashin da akan tatso gaga tsirrai wajen hakar kudin na Bitcoin da hada-hadarsa, musamman ma kwal, wanda yak e fitar da gurabaciyar iska fiye da sauran makamashi,'' Mr Musk ya wallafa.

"Kudaden intanet, tunani ne mai kyau… amma kuma hakan ba zai zama abinda za mu bari ya gurbata muhalli ba."

Ya ce kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki bai yi nufin sayar da ko da daya daga cikin Biticoin din sa ba amma ya yi aniyar sake dawo da hada-hadar kudin na intanet da zarar hakar ma'adinan ta sauya zuwa amfani da ingantaccen makamashi mai dorewa.

Duk da cewa ba zai yiwu a yi kasuwacin kudaden intanet din ba a kasar China, fiye da kasha 75 bisa dari (75%) na hakar Bitcoin a fadin duniya ana yin shi ne a kasar ta China.

Sharhi daga Rory Callen-Jones wakilin BBC kan harkokin Fasaha

Ga duk wanda ya jima yana bibiyar batutuwan da suka shafi kudin intanet, abubuwan da suka faru a makonnin baya-bayan nan labari ne da aka sani.

Wasu abubuwa da suka faru lokaci guda - sun ce, sanarwar da Elon Musk ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kamfaninsa na Tesla zai amince da kudin Bitcoin wajen sayen motocinsa - ya kara wa Bitcoin din tagomashi, daga nan sai mutane suka ce abu ne da zai samu karbuwa daga jama'a.

Bayan nan kuma wani abu ya sake faruwa, mai yiwuwa wani sauyi ko shakka babu daga jagoran kamfanin na Tesla. Batun ya sauya alaka zuwa baya kuma.

A watan da ya gabata, a wani dakin tattauna wa, na nuna wasu-wasina game da kudaden na intanet.

Amma a cikin wannna makon, yanayin ya sauya, inda jaridar Finacial Times ta bayar da rahoton ''sabbin wasu-wasi a tsaanin manajojin kamfanonin hada-hadar kan makomar kudaden na intanet a matsayin wata kadara''.

Tunani na ya koma baya a shekarar 2013, lokacin da n afara nuna sha'awata ta farko ga Bitcoin.

A wani rahoto ga shirin yamma na sashen Radio 4, na sayi haddaen burodin pizza kan kudin Bitcoin 0.5, wanda darajar shi ta kai fan talatin (£30) - wanda ko shakka babu a yanzu darajar canjin kudin ta kai fan dubu sha hudu (£14,000) pizza.

Na kuma yi rubuce-rubuce ta shafin intanet da na yi masa babban lakabi da ''Garabasar Bitcoin'' inda na yi kokarin koyar wasu darusaa daga lokacin da farashin kudin na intanet suka kara hauhawa daga dala 15 zuwa dala 276, kana suna sake subutowa kasa.

Na karkare rubutuna a inda na kwatanta kudin intanet da furannin tulip na Dutch na karni na 17, da kuma gidajen birnin London a cikin shekarar 1980 da wannan tunani: "Muddin ba za a iya amfani da Bitcoin waejn sayen hadden burodin sandwich, ko kuma abokan ka su amince da shi idan ka biya su kudin abincin da kuka ci a gidan cin abinci, to kuwa akwai yiwuwar ya cigaba da kasancewa tamkar wani abin wasa ka 'yan caca da masu raye-rayen gargajiya.''

Bayan shekaru takwasa, har yanzu ya kasance ta wahala ka je ka sayi hadadden burodin sandwich da Bitcoin.

Kuma ma me zai sa ka yi hakan, tun da akwai yiwuwar a rika zolayarka bayan shekaru kadan - kan bayar da wata kadarar da daraajarta ke kara yin kasa?