Jurgen Kloop ya ce da kayr ne idan Liverpool za ta kammala gasar Premier League ta bana a cikin 'yan hudun farko.
Duk da cin Woles da Liverpool ta yi ranar Lahadi, shi ne wasa na hudu da ta yi nasara tun cikin watan Kirsimeti.
Duk da haka saura maki biyar ta tarar da Chelsea wadda take ta hudu a teburi, sai kuma ta haura West Ham ta biyar da tazarar maki biyu tsakani.
Liverpool ta buga wasan mako na 29 a Premier League a bana da maki 46, West Ham kuwa mai kwantan wasa ta yi karawa 28 kawo yanzu.
Everton wadda take ta bakwai a teburi, maki iri daya ne da ita da na Liverpool da zarar maki daya tsakaninsu da Tottenham ta takwas.
"A dai kakar bana da kyar ne idan za mu samu gurbin shiga gasar Champions League ta bana ta hanyar kammala Premier cikin 'yan hudun farko"
Kamar yadda Kloop wanda Liverpool ta kai wasan quarter finals a Champions League na bana ya sanar da jaridar Bild a wata hira da ta yi da shi.
"A Tottenham, Gareth Bale na bayar da gudunmuwa suna kuma cikin 'yan takarar hudun farko, yayin da Manchester City da United sun yi mana nisa.
"Mun kwan da sanin kokarin da Chelsea ke yi tare da sabon koci, sun kuma kai wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League.
"Ba za ka iya lashe Champions League a shekara idan kana da 'yan wasa da dama da ke jinya kamar yadda ya faru damu tun farko farkon kakar bana.
Kloop ya ce hanyar da ta ragewa kungiyar ita ce lashe kofin zakarun Turai na bana, shima sai da rabo ba tabbas.
Sai dai kocin ya kara da cewar tabbas idan Liverpool ba ta samu gurbin shiga Champions League na badi ba, kudin shigar kungiyar zai yi kasa kuma hakan ba abu ne mai kyau ba.
Sai dai ya kara da cewar baya fargabar zai rasa aikinsa koda Liverpool ba ta kai gasar zakarun Turai ba yana sa ran ci gaba da zama a Anfield.
Liverpool ta samu gurbin buga gasar quarter finals a Champions League na bana da za a raba jadawalin wasannin gaba ranar Juma'a.
Sauran kungiyoyin da suka kai bantensu sun hada da Chelsea da Manchester City ta Porto da Borussia Dortmund da Paris St Germain da Real Madrid da mai rike da kofin Bayern Munich.
A kakar bara Liverpool ta lashe kofin Premier League da tazarar maki 18, kuma a karon farko tun bayan shekara 30 rabonta da shi.
Liverpool za ta ziyarci Arsenal ranar 4 ga watan Afirilu domin buga wasan Premier League karawar mako na 30.