Wannan muƙala ce daga baƙonmu na wannan makon Muhammad Bala Garba, Ɗalibi a Jami'ar Maiduguri, kan asalin wasan Barebari da Fulani.
Akasarin Barebari (Kanurai) da Fulani ba su san tarihin wasan da ke tsakaninsu da juna ba, illa dai kawai sun tashi sun ga iyayensu da kakaninsu suna wasan zolayan juna idan an haɗu.
Wannan ya sa naga dacewar bincikowa 'yan uwana Barebari da Fulani tarihin wasan da ke tsakaninsu. Na ciro wannan bayanin ne daga littafin 'ƘASAR BARNO A JIYA' da ni Muhammad Bala Garba, Maiduguri na wallafa.
Wasan da ke tsakanin Barebari da Fulani Tarihi ya nuna cewar bunƙasar shahararriyar Daular Borno ta Kanurai ta soma yin ƙasa ne tun bayan rasuwar Sarkinsu Mai Idris (Aloma) a wuraren ƙarni na 17 zuwa na 17.
Don haka ya zamana daular ta dinga asarar manyan garuruwan da suke ƙarƙashinta sakamakon yadda ƙarfin ikonta ke durƙushewa.
Ana wannan yanayi, sai kuma Fulani suka soma jihadi a shekarar 1804 Miladiyya. Don haka bayan yaƙe-yaƙensu ya yi ƙamari, sai ya zamana suna tashi zuwa garuruwa domin cinsu da yaƙi, sai da ta kai har masarautar Borno sun riska da yaƙi.
A shekarar 1808 ne Fulani suka ƙwace cibiyar Masarautar Borno da ke garin Ngazargamu, inda suka ƙone garin tare da korar mayaƙan garin.
A shekarar 1814 kuma sai babban Malami a Daular Borno mai suna Shaihu Muhammadul Amin El-kanemi ya jagoranci kafa sabuwar Daular Barno a wani gari mai suna Kukawa.
Sannan ya haɗa runduna gami da soma taimakon sarkinsu mai suna Mai Dunama Lefiagi.
Daga baya, bayan sarki Mai Dunama ya so hallaka Shaihu Muhammadul Amin El-kanemi saboda hassadar farin jininsa a wurin jama'a, amma bai samu nasara ba, sai Shaihu Muhammadul Amin El-kanemin ya zamo sarkin Borno mai cikakken iko ba tare da zub da jini ba.
Don haka ya shiga ƙalubalantar Fulani da suka hana su sakat ta hanyar yaƙarsu da kuma aike wa da wasiƙun ilimi yana tuhumar Shugaban Fulani, wato Mujaddadi Shehu Usman Dan Fadiyo a kan cewa don me zai shiga yaƙi da Daular Borno, alhali ta fi shekaru 800 da karɓar addinin Musulunci kuma da sunan yaƙin Musulunci.
To, a haka dai aka dinga gwabzawa da yaƙi da kuma rubuce-rubuce na wasiƙu har zuwa rasuwar Mujaddadi Shehu Usman Ɗan Fodio, yayin da ɗansa Muhammadu Bello ya gaje shi a shekarar 1826 inda yaƙi ya ƙara ƙamari a tsakaninsu.
Babu jimawa kuma bayan kowa ya sha wuya a hannun ɗan uwansa, sai kuma aka yanke shawarar yin maslaha. Anan aka yi sulhu, aka bar Kanurai (Barebari) da birninsu, amma dai sun rasa ikon wasu yankunan da a baya suke hannunsu izuwa hannun Fulani.
Inda wasan ƙabilu ya shigo
A inda wasan ƙabilun biyu ya shigo shi ne, dirkakowar mayaƙin nan daga ƙasar Sudan zuwa yankin Borno, wato Rabeh Zubair Ibn Fadlallah.
A cikin shekarar 1893 Rabeh ya zo daga Sudan da shiri na gaske, ya afka wa Daular Borno da yaƙi, nan da nan ya yi karin kumallo da ita. Rabeh da mutanensa sai abin da suka ga dama suke a Borno.
Wani yaƙi da aka yi a kusa da Farlomi, sojojin Faransa na mulkin mallaka suka kashe Rabeh bayan ya yi mulki a shekaru bakwai da watanni bakwai da kwanaki bakwai a Borno.
Bayan lokaci kaɗan sai Ingilishi suka ci ƙasar da yaƙi, suka mayar da zaman lafiya da salama.
Wuyar da Kanurai suka sha a hannun Rabeh, wanda ya zamo rabinta ba su sha ba a yaƙinsu da Fulani, shi ya sa Fulani suke tsokanarsu idan sun gansu, suke cewa, "Ga Rabeh nan," su kuwa Barebari sai kaga sun hargitsa kamar ɓera ya hango kyanwa.
Daga baya da Barebari suka gane tsokana ce kawai, sai suma suke mayar da martani, har kuma abin ya zamo wasan tsokana tsakanin waɗannan ƙabilu biyun.
Amma dai har izuwa yau, Barebari sun yadda su sanyawa 'ya'yansu sunan Usmanu, amma ba sa sanyawa 'ya'yansu sunan Rabeh ko Rabi'u.
Wannan shi ne tarihin wasan da ke tsakanin Barebari da kuma Fulani. Akwai bayani iya bakin gwargwadona game da tarihin ƙasar Barno, suna da asali, da kuma wasu daga cikin kyawawan halayen Barebari da abin da ya shafe su a cikin littafin "ƘASAR BARNO A JIYA."
Da wannan na zo ƙarshen wannan muƙalar tawa. Ina roƙon Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki ya albarkaci wannan aikin namu, ya sa ya amfani dukkan ɗaliban ilimi.
A ƙarshe ina sake roƙon Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki ya haɗa kanmu, ya ba mu zaman lafiya mai ɗaurewa a yankinmu na Arewa.
Daga Mohammed Bala Garba, ɗalibi a jami'ar Maiduguri. Za a iya samunsa a waɗannan lambobin. 08098331260, 08025552507.