Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta tsakanin hamshaƙan ƴan kasuwar Najeriyar nan biyu ƴan asalin jihar, Alhaji Aliko Ɗangote da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u kan saɓanin fahimtar da suka samu a baya-bayan nan.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamnan Ganduje ya ce an yi zaman sulhun ne tsakanin jami'an gwamnatin jihar da wasu manyan masu faɗa a ji da kuma ƴan kasuwar ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce rikicin na baya-bayan nan ya samo asali ne tsakanin manyan masu arzikin biyu kan batun farashin sikari a kasuwar Najeriya.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Dangote ya zargi BUA da amfani da wata dama ta hanyar da ba ta dace ba, yayin da shi kuma Abdussamad ya ce yana so ya mamaye kasuwar ne ya kuma dinga sa farashi yadda ya ga dama.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata, Dangote ya yi watsi da zargin sanya farashin da ya ga dama.
Sanarwar ta ce "wannan tataɓurza da ake ta yi ce ta sa Gwamna Ganduje ya gayyaci 'yan kasuwar biyu kasancewar su 'yan asalin jihar Kano da kuma irin gudunmawar da suke bai wa jihar da ƙasa baki ɗaya."
Amma a zaman da aka yi da 'yan kasuwar da gwamnatin Kano, sun tabbatar da cewa babu ƙamshin gaskiya a kan maganar da ake yaɗawa cewa, Aliko Dangote ya nemi Abdussamad Isyaka Rabi'u domin su yi ƙarin kuɗin sikari, inda suka tabbatar da cewa wannan zance ba shi da asali.
A yayin zaman sulhun dai manyan ƴan kasuwar biyu sun tabbatar da cewa za su wadata Najeriya da sikari.
Cikin manyan mutanen da suka halarci sulhun har da hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda kawu ne ga Aliko Dangote.
Sannan akwai Ministan Ciniki da Masana'antu Niyi Adebayo da Wakilin Kano, Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Dan Agundi da shugaban hukumar NEPZA Adamu Fanda da kuma shugaban majalisar limaman Juma'a kuma limamin masallacin Ahmadu Tijjani da ke Ƙofar Mata wato Sheikh Nasiru Adam.
"Bayan tattauna muhimman batutuwa da jan hankali da Gwamna Ganduje da kuma Aminu Dantata suka yi, an samu daidato da fahimtar juna tsakanin manyan yan kasuwar biyu, inda suka yi alƙawarin ɗinke duk wata rashin fahimtar juna da ke tsakanin su," a cewar sanarwar.
Aliko Dangote shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka sannan shi da Abdussamad Isyaka Rabi'u abokai ne.
Duk da cewa mutanen biyu ƴan asalin jihar Kano ne, amma sun fi yin harkokin kasuwancinsu a jihar Legas da ke kudu masu yammacin Najeriya.