A karon farko kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta lashe kofin FA a tarin kafuwarta.
Youri Tielemans ne ya jefa kwallo daya tilo wadda ta bai wa Leicester samun nasara kan Chelsea da kuma damar lashe wannan kofi a filin wasa na Wembley.
Wani tsautsayi ne aka samu a bayan Chelsea wanda yakai ga bai wa dan wasan Leicester kwallo a lafarsa kuma ya buga daga wajen yadi na 25 a minti ba 63 ta wuce mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga ta fada koma.
Sai da kocin kungiyar Brendan Rodgers yaje har kasa domin murna, kuma dama a filin wasan akwai magoya baya da aka bari suka shiga domin kallo.
Magoya baya 21,000 aka bari suka shiga Wembley a karon farko tun bayan sanya dokar korona da kuma dakatar da magoya baya shiga kallo.
Mai tsaron ragar kungiyar Foxes Kasper Schmeichel ya kankaro su bayan turo wasu kwallaye da ya yi har biyu.
A daf da tashi ne kuma dan bayan Chelsea Chilwell ya samu damar farke kwallon a mintinan karshe na wasan, amma bayan an duba na'urar taimakawa alkalin wasa na gano cewa yayi satar gida, aka kuma soke kwallon.
Wannan rashin nasara bai yi wa Chelsea dadi ba, kuma a gaban wasu daga cilkin magiya bayanta da suka shiga kallon wannan wasa.
A yanzu haka dai Chelsea za ta buga wasanta na karshe a gasar zakarun Turai da Manchester City.
Da farko dai an tsara buga wannan wasa ne a Turkiyya, amma karuwar masu kamuwa da cutar korona a kasar ta sanya hukumomi suka nemi a dawo da wasan Burtaniya, amma daga baya an mayar da shi Portugal.
Chelsea da na matsayi na hudu ne a gasar Premier da maki 64 a saman Liverpool da West Ham, tana kuma biye wa Leicester da ke samanta da maki biyu kacal.