Fadar shugaban Najeiya ta yi zargin cewa wasu tsoffin shugabannin siyasa da malaman addini suna yin markashiyar da za ta kai ga kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya aike wa manema labarai ta ce mutanen suna son kawo yamutsi a kasar ne sanna su yi amfani da damar wajen kifar da gwamnatin.
"Ranar Lahadi Hukumar tsaron farin kaya ta (DSS), ta jawo hankali game da muguwar aniyar wasu da ke son hargitsa gwamnati da dorewar kasar.Wasu malaman addini da tsoffin masu rike da mukaman siyasa da da ba sa kishi ne suke gaba-gaba, kuma manufarsu ita ce daga karshe kasar ta fada cikin rikici, wanda zai tilasta sauya shugabancin zuwa wanda ba na dimokradiyya ba," in ji Mr Adesina.
Ya kara da cewa wasu hujjoji masu kwari sun nuna cewa wadannan mutanen suna daukar nauyin shugabannin wasu kabilu da 'yan siyasa a duk fadin kasar, bisa niyyar gudanar da tarukan da za su yi Allah-wadai da shugaban kasa, lamarin da zai kara jefa kasar cikin yamutsi.
A cewarsa, wasu mutane sun rika gudanar da wasu abubuwa da zummar share hanya wajen jefa kasar cikin hargitsi.Kakakin na Shugaba Buhari ya ce manufar mutanen ita ce cimma burinsu wanda suka gaza samu a lokacin zaben 2019.
Sai dai ya kara da cewa 'yan Najeriya sun zabi a yi musu mulki na dimokradiyya kuma ba za su amince da wani mulki ba idan ba na dimokradiyyar ba.
'Mun daina kawar da kai'
A karshen makon jiya ne Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) ta bayyana cewa daga yanzu ba za ta kawar da kai daga wasu mutane da ke neman tayar da zaune tsaye a kasar ba.
DSS ta soki abin da ta kira wasu kalamai na marasa son zaman lafiya da ke barazana ga gwamnati da dorewar kasar.
"Abin da ya ja hankalinmu shi ne kalaman da ba su dace da kuma wasu ayyukan malaman addini da shugabannin siyasa da suka gabata wadanda ko dai suka yi kira a cire gwamnati da karfi ko kuma suke so a yi tarzoma. Mun gano cewa sun yi hakan ne domin kawo rashin zaman lafiya," a cewar DSS.
Hukumar ta kara da cewa abin takaici ne mutanen da ake gani da kima suna yin irin wadannan kalamai domin biyan bukatun kashin kansu.
"Muna masu tuna musu cewa kodayake mulkin dimokradiyya ya bayar da 'yancin fadar albarkacin baki, amma ba ta bayar da damar yin kalamai na ganganci da ka iya shafar tsaron kasa ba," in ji hukumar ta DSS.
'Cin amanar kasa'
A nata bangaren, rundunar sojin Najeriya ta yi gargadi ga masu kira a gare ta domin ta kwaci mulki daga hannun gwamnatin farar hula da su kiyaye ta.
Rundunar ta yi gargadin ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafinsu na intanet.
Ya ce sojoji ba za su sanya kansu cikin lamarin da zai gurgunta mulkin dimokradiyya ba, yana mai karawa da cewa za su murkushe duk wani yunkuri na kifar da gwamnati.
"An jawo hankalin manyan jam'an soji bisa kalamin da wani da ake kira Robert Clark SAN ya yi, inda yake bayar da shawara cewa jagororin mulkin siyasa su mika mulki ga sojoji domin sauya fasalin kasar nan. Rundunar sojin Najeriya tana mai tsame kanta daga wannan kalami da ya ci karo da tsarin dimokradiyya," in ji Birgediya Janar Nwachukwu.
Ya kara da cewa rundunar sojin Najeriya tana "son yin amfani da wannan dama domin ta gargadi 'yan siyasar da ba su da alkibla wadanda ke son mulkin kasar nan ba ta hanyar zabe ba da su guji yin irin wannan tunani" domin a shirye sojoji suke su kare kasar.
"Muna son tuna wa dukkan jami'an soji cewa yin tunanin juyin mulki laifi ne na cin amanar kasa. Za a hukunta duk wanda aka samu ya hada baki wajen aiwatar da irin wannan shiri," a cewar Birgediya Janar Nwachukwu.
Kakakin rundunar sojin ta Najeriya ya ce matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar abubuwa ne da za a iya shawo kansu yana mai cewa suna hada gwiwa da sauran jami'an tsaro wajen magance su.